Saura Kwanaki 2: Abubuwan da Dalibai za su Tanada Kafin Samun Lamunin Karatu
Nan da kasa da kwanaki biyu daliban Najeriya za su fara samun damar neman lamunin karatu daga gwamnatin tarayya karkashin asusun bawa daliban kasar nan rance da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta bijiro da shi.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Shirin gwamnatin tarayya na tallafawa marasa galihu a kasar nan da bashin ilimi, gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta gindaya sharuddan da sai an cika su za a samu damar karbar rance.
Asusun bayar da bashin na NELFUND a wani taro da ya gudanar ranar Litinin ya zayyana hanyoyin da za a bi wajen neman rancen har a dace, kamar yadda The Cable ta wallafa.
Matakan karbar rancen karatu
Ga jerin matakan da daliban Najeriya su bi domin neman rancen kamar yadda Darakta Janar na asusun, Akintinude Sawyerr, ya bayyana;
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Shiga shafin NELFUND
Da fari dai daliban da ke da sha’awar karbar rancen za su ziyarci shafin asusun NELFUND na www.nelf.gov.ng. A nan ne za a shiga bangaren neman rancen dalibai.
2. Samar da asusun neman rance
Bayan dalibi ya shiga shafin ne sai kuma ya samar da asusun sa a ciki da ke nuna shi dalibi ne ko ya shiga kai tsaye idan da ma ya taba budewa.
A nan ne mai neman rancen zai cike dukkanin bayansa ciki har da halin da aljihunsa ke ciki.
3. Abubuwan da za a bukata
A wannan matakin ne dalibi mai neman rance zai yi amfani da wasu bayanai da su ka hada da takardar daukarsa karatu da hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu ta JAMB ta ba shi.
Sai kuma shaidar zama dan kasa ta NIN da na banki watau BVN.
4. Aikewa da neman rancen ilimi
Idan dalibi ya kammala dukkanin matakai ne kuma sai ya sake bibiyar abin da ya rubuta domin tabbatar da ya shigar da bayanansa daidai.
Daga nan kuma sai a aike da bukatar neman rancen a kuma jira.
Tun a watan Afrilun 2023 shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan dokar ba dalibai rancen, amma a yanzu ne ake sa ran za a fara ba daliban.
Iyaye sun koka kan rancen karatu
A baya mun kawo mu ku labarin cewa wasu iyaye da dalibai sun koka kan gyaran fuskar da gwamnatin tarayya ta yiwa shirin ba da rancen karatu da za a fara a kasa da kwanaki biyu masu zuwa.
Shugaban dalibai jam'a ta kasa (NAUS) Kwamared Obaji Marshall na ganin ko kodan gwamnati ba ta kyauta da yiwa tsarin kwaskwarima ba.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng