‘Banex Plaza’: Soja Ya Shararawa Wata Mata Mari Har Ta Fada Doguwar Suma

‘Banex Plaza’: Soja Ya Shararawa Wata Mata Mari Har Ta Fada Doguwar Suma

  • Rahotanni sun bayyana cewa wani soja ya shararawa wata mata mari a kan titin babban kantin Bannex da ke Abuja
  • An ce karfin marin ya zubar da matar kasa inda ta fada doguwar suma, yayin da aka saka ta a mota aka bar wajen da ita
  • Wannan na zuwa ne yayin da sojoji suka rufe babban kantin biyo bayan lakadawa jami'ansu duka da aka yi kwanan baya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Daya daga cikin jami’an soji da ke sa ido a babban kanti na Banex da ke unguwar Wuse 2 a Abuja, ya mari wata mata har ta fada doguwar suma.

Akalla kwanaki hudu kenan da babban kantin Bannex ke a kulle bayan wasu ‘yan daba sun lakada wa wasu sojoji dukan tsiya saboda sun samu rashin jituwa da wani dan kasuwa.

Kara karanta wannan

Lauyoyin Murja sun yi fatali da ita, sun fadi nadamar da suka yi a shari'arta

Wani soja ya shararawa wata mata mari a Abuja
Soja ya shararawa wata mata mari har ta suma a Abuja.
Asali: Twitter

Soja ya shararawa wata mata mari

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa wakilinta ya je yankin da kantin ya ke a lokacin da sojan ya mari matar bayan ta tsallaka shingen da suka saka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matar tana tafiya ne a kan hanyar da sojojin suka hana a bi, lamarin da ya sa jami'an suka tare ta.

Bayan an yi mata wasu tambayoyi ne sai daya daga cikin sojojin ya mare ta da karfi inda ta fadi kasa nan take.

An saka matar a cikin mota

Wakilin jaridar da ke a wurin ya shaida yadda aka dauki matar aka saka ta a cikin wata mota kirar 'van' da sauri.

Babu tabbas ko an kai ta asibiti domin kula da lafiyarta ne.

A halin da ake ciki dai, ‘yan kasuwa na ci gaba da kirga asarar da suka yi kan matakin da sojoji suka dauka, wanda a cewarsu za a iya magance su ba tare da an rufe shagunan ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.