Fitattun 'Yan Arewa Guda 5 da Bola Tinubu Ya ba Manyan Mukamai a Jami’o’i
- A makon da ya wuce shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada mutane 555 a manyan makarantu 111 a fadin Najeriya
- Mutanensu 555 za su rike shugabancin kwamitocin gudanarwa na jami'o'i da kwalejojin ilimi da fasaha da ke cikin kasar
- Legit ta tattaro muku sunaye da takaitaccen tarihin fitattun yan Arewa 5 da suka samu shugabancin kwamitocin ko zama mambobi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Arewa - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada yan Najeriya mutum 555 domin rike shugabancin kwamitocin manyan makarantu a Najeriya.

Asali: Facebook
Mutanen sun hada da yan siyasa, masu sarautar gargajiya, ma'aikatan gwamnati, yan kasuwa da sauransu.
Mai taimakawa shugaban kasa a harakar yada labarai, Bayo Onanuga ya wallafa sunayen mutanen a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu: 'Yan Arewa da aka ba muƙamai
1. Farfesa Attahiru Jega
Shugaban kasa ya nada Farfesa Attahiru Jega shugabancin kwamitin gudanarwa na jami'ar Usman Dan Fodiyo da ke Sokoto.

Asali: Facebook
An haifi Farfesa Jega a shekarar 1957 a jihar Kebbi, ya kuma yi karatu a jami'o'in ABU Zariya da BUK kano.
Jega ya yi aiki a jami'ar Bayero inda tun daga malanta sai da ya dawo mataimakin shugaban jami'ar. A shekarar 2010 tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya nada shi shugaban hukumar INEC.
2. Isa Yuguda
Bola Ahmed Tinubu ya nada Isa Yuguda a matsayin shugaban kwamitin gudanarwa na jami'ar NOUN da ke gudanar da karatu ta yanar gizo.

Asali: Facebook
An haifi Isa Yuguda a shekarar 1956 a jihar Bauchi. Ya kuma yi karatu a jami'o'in ABU da Jos.

Kara karanta wannan
Sheikh Pantami ya aiko ta'aziyya yayin da aka rasa daya daga cikin dattawan Gombe
Isa Yuguda ya kasance gwamna a jihar Bauchi na shekaru takwas kuma Olusegun Obasanjo ya nada shi ministan sufuri a lokacin da ya ke shugaban kasa kuma gogaggen tsohon ma'ikacin banki ne.
3. Dakta Aliyu Tilde
Shugaban kasa ya nada Dakta Aliyu Tilde mamba a kwamitin gudanarwar jami'ar gwamantin tarayya da ke Dutsim-ma a jihar Katsina.

Asali: Facebook
Dakta Tilde ya fito daga jihar Bauchi kuma gogaggen marubuci ne da ya shafe shekaru yana rubuce-rubuce a jaridu dabam-dabam.
Ya kuma rike mukamai daban daban a Najeriya daga cikinsu akwai kwamishinan ilimi a jihar Bauchi.
4. Alhaji Mahmud Yayale Ahmed
Shugaba Bola Tinubu ya nada Alhaji Yayale Ahmed shugaban kwamitin gudanarwa a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Asali: Facebook
An haifi Yayale Ahmed a shekarar 1952 a jihar Bauchi. Ya kuma yi karatu a jami'ar ABU Zariya da jami'ar Abuja.
Ya rike manyan mukamai cikinsu akwai ministan tsaro da shugaban ma'aikatan gwamnatin tarayya a lokacin mulkin Obasanjo.
5. Mahmud Aliyu Shinkafi
An ba Mahmud Aliyu Shinkafi mukamin shugaban kwamitin gudanarwa a jami'ar jihar Filato da ke birnin Jos.

Asali: Facebook
An haifi Mahmud Aliyu Shinkafi a shekarar 1960 a jihar Zamfara. Ya kuma zama gwamnan jihar jami'ar ANPP amma daga baya ya canza sheka.
Tinubu ya ba da sababbin mukamai
A wani rahoton, kun ji cewa shugaba Bola Tinubu ya yi sababbin nade-nade a manyan hukumomi biyu a ranar Juma'a 19 ga watan Afrilu a Abuja.
Shugaban ya nada Mista Mairiga Aliyu a matsayin shugaban kwamitin hukumar SEC sai Halima Kyari a matsayin shugaba hukumar NAICOM.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng