Gwamna Ya Shiga Yanayi Yayin da Ƴan Bindiga Suka Kashe Sojojin Najeriya

Gwamna Ya Shiga Yanayi Yayin da Ƴan Bindiga Suka Kashe Sojojin Najeriya

  • Gwamna Alex Otti ya yi jimamin mummunan harin da aka kashe sojoji biyu a Aba ta jihar Abia tare da alƙawarin kamo masu hannu a laifin
  • Rahotanni sun nuna cewa ƴan bindigar sun kashe mutune uku a harin gabanin dakarun sojoji su yi nasarar fatattakar su
  • Wannan harin ya faru ne ƙasa da shekara ɗaya bayan ƴan bindiga sun kai hari sansanin sojojin Aba, duk da dai babu wanda ya rasa ransa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Abia - Gwamna Alex Otti na jihar Abia ya miƙa sakon ta'aziyya ga rundunar sojojin Najeriya bisa mummunan harin da ƴan bindiga suka kai wa sojoji a Aba.

Ƴan bindigar sun hallaka dakarun sojoji biyu da kuma wani mai Keke Napep a harin da suka kai kai jihar Abia da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.

Kara karanta wannan

Congo: An shiga fargaba yayin da aka yi yunkurin juyin mulki, an yaɗa bidiyon

Gwamna Alex Otti na Abia.
Gwamna Otti ya ziyarci wurin da ƴan bindiga suka kashe sojoji a Abia Hoto: Alex Otti
Asali: Facebook

Sojoji sun daƙile harin Aba

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa dakarun sojojin da ke shingen binciken Aba, sun samu nasarar daƙile harin tare da fatattakar ƴan bindigar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shaidun gani da ido da suka hada da wani mai a-daidaita-sahu mai suna Chima Ibekanma, sun ba da labarin firgici da hargitsin da mutane suka shiga a yayin harin.

A cewarsu, soja ɗaya ya mutu nan take yayin da ɗayan kuma ya cika a asibiti bayan munanan raunukan da ya samu, jaridar Vanguard ta rahoto.

Lamarin dai ya kawo cikas ga harkokin kasuwanci a yankin, inda masu motocin bas na haya suka kasa lodin fasinjoji saboda matakan tsaron da sojoji suka dauka.

Wannan harin na zuwa ne ƙasa da shekara guda bayan wani hari makamancin haka da aka kai a sansanin soji a garin Aba, ko da yake babu wanda ya mutu a wancan lokacin.

Kara karanta wannan

Ana murnar Notcoin ya fashe, kotun tarayya ta yanke hukunci kan jami'in Binance a Najeriya

Gwamnatin Abia na tare da sojoji

Gwamna Otti, bayan ya duba wurin da lamarin ya faru, ya yaba wa sojojin tare da yin alkawarin cewa gwamnatinsa za ta ba da goyon baya wajen kamo masu hannu a harin.

Birgediya Janar O.O.Diya na runduna ta 14, ya bai wa gwamnan tabbacin ci gaba da kokarin damke wadanda suka aikata wannan aika-aika, wadanda suka tsere a yanzu.

Sojoji sun ceto mutane a Sambisa

A wani rahoton kuma Sojojin Najeriya sun yi nasarar ceto wasu mutanen da ‘yan ta’adda suka sace tsawon shekaru 10 zuwa yanzu

An bayyana sabon aikin da sojojin suka fara domin tabbatar da sun kakkabe dajin Sambisa daga masu aikata ta’addanci a Arewa maso Gabas.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262