Mummunar Gobara Ta Tashi a Makarantar Addini Ta Najeriya, Dalibi 1 Ya Mutu
- Mutum daya ya mutu yayin da kadarori suka kone a wata gobara da ta tashi a makarantar Bishop Crowther Memorial, Anambra
- Kodayake har yanzu ba a san musabbabin tashin gobarar ba, an tattaro cewa lamarin ya faru ne a daren ranar Asabar
- Shugaban hukumar kashe gobara na jihar, Chukwudi Chiketa, ya ce an kai gawar dalibin da ya mutu zuwa dakin ajiyar gawa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Anambra - Wata gobara da ta tashi da tsakar dare ta yi sanadiyyar mutuwar dalibi daya tare da lalata kadarori a makarantar Bishop Crowther Memorial da ke Awka a jihar Anambra.
Dalibi 1 ya mutu a gobarar
Har yanzu dai ba a gano musabbabin abin da ya jawo tashin gobarar a ranar Asabar ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gobarar ta lalata dakunan kwanan dalibai da suka hada da katifu da sauran kayayyakin daliban, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.
An ruwaito cewa an kai wani dalibi da ya mutu a lamarin zuwa dakin ajiyar gawa.
Sashen yada labarai na hukumar kashe gobara ta jihar Anambra da ke Awka ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa.
Hukumar kashe gobara ta magantu
Shugaban hukumar kashe gobara na jihar, Chukwudi Chiketa, ya ce an tura jami’ai da motar kashe gobara bayan faruwar lamarin kuma an shawo kan wutar.
Channels TV ta ruwaito cewa Chiketa ya ziyarci makarantar a ranar Lahadi, inda shugaban makarantar ya bayyana yadda gobarar ta shafi wani bangare na dakin kwanan dalibai.
Shugaban hukumar ya jajanta ma mahukuntan makarantar da daukacin daliban, da kuma iyalan dalibin da ya rasu.
Hatsarin jirgin da ya kashe shugaban Iran
A wani labarin, mun ruwaito cewa babu wanda ya tsira a hatsarin jirgin sama da ya rutsa da shugaban kasar Iran, Ebrahim Raisi da mukarrabansa a ranar Lahadi.
Mun tattaro muhimman abubuwan da ya kamata ku sani game da hatsarin da kuma abubuwan da suka faru a Iran bayan mutuwar shugaban kasar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng