Wuta bal-bal: Gobara ta kama a dakin kwanan dalibai mata na wata makaranta a Abuja

Wuta bal-bal: Gobara ta kama a dakin kwanan dalibai mata na wata makaranta a Abuja

- Gobara ta kama a dakin kwanan dalibai mata na wata makaranta a Abuja

- Da dare wajen karfe 10 na daren ranar Larabar da ta gabata ne lamarin ya auku

- Shugaban hukumar dake kula da makarantun kwanan garin na Abuja ya tabbatar da hakan

Wata gobara da ta tashi da tsakar dare a makarantar kwana da Sakandiren 'yan mata ta Government Secondary School (GSS) Kuje, dake garin Abuja ta ja wa dalibai da dama asara ta dumbin dukiya.

Wuta bal-bal: Gobara ta kama a dakin kwanan dalibai mata na wata makaranta a Abuja
Wuta bal-bal: Gobara ta kama a dakin kwanan dalibai mata na wata makaranta a Abuja
Asali: UGC

KU KARANTA: An hurowa sabon shugaban DSS wuta ya saki Zakzaky da Dasuki

Wata dalibar makarantar da ta zanta da wakilin majiyar mu ta shaida mana cewa wutar ta soma ci ne da dare wajen karfe 10 na daren ranar Larabar da ta gabata.

Legit.ng ta samu daga dalibar haka zalika cewa gobarar ta soma ne sakamakon guga da dutsen guna na garwashi da wata daliba ke anfani da shi.

Haka zalika, shugaban hukumar dake kula da makarantun kwanan garin na Abuja, watau FCT Secondary Education Board (SEB) mai suna Alhaji Musa Yahaya Muhammad ya tabbatar da faruwar lamarin.

A wani labarin kuma, Dakarun sojin Najeriya tuni sun soma aikin zuke tafkunan wasu garuruwa da kauyukan karamar hukumar Jos ta kudu dake a jihar Filato a cigaba da zurfafa binciken neman gawar dan uwan su da ya bace a kwanan baya.

A baya dai mun kawo maku labarin cewa wani babban jami'in rundunar sojin ta kasa mai suna Manjo Janar Idris Alkali ya bata a kan hanyar sa ta zuwa Bauchi daga garin Abuja.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng