Yanzu-yanzu: Gobara ta cinye dakunan kwanan dalibai a makarantar kwana a Kaduna

Yanzu-yanzu: Gobara ta cinye dakunan kwanan dalibai a makarantar kwana a Kaduna

Hankula sun tashi a makarantar sakandarin gwamnati ta mata, GGSS da ke Kawo a Kaduna sakamakon gobara da ta lashe dakunan matan dalibai biyu.

Dakunan kwanan da gobarar ta shafa su ne Nana House da Khadija House inda dukkan katifu da kayan masaruhi na daliban suka kone kurmus.

Daily Trust ta gano ruwaito cewa har yanzu ba a san ainihin abinda ya yi sanadin gobarar ba.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa dakin daliban na farko ya kone misalin karfe 9 na safe yayin da na biyun kuma ya yi kone da yammacin ranar.

Majiyar ta kuma ce iyayen dalibai da dama sun kwace 'ya'yansu daga makarantar duk da cewa hukumar makarantar da bukaci a dawo da daliban inda ta ce ta magance lamarin a yanzu.

Yanzu-yanzu: Gobara ta cinye dakunan kwanan dalibai a makarantar kwana a Kaduna
Yanzu-yanzu: Gobara ta cinye dakunan kwanan dalibai a makarantar kwana a Kaduna
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Matsala ce mai nasaba da tsarin kundin mulki - Ganduje ya yi magana a kan Sarki Sanusi II

Wani mahaifin wata daliba mai suna Alhaji Suleiman ya ce, "Sun fara samar wa daliban katifu amma har yanzu babu wanda ya fada mana abinda ya yi sanadin gobarar. Dakunan kwanan dalibai biyu sun kone kurmus amma babu wanda ya rasa rai."

Da ya ke tabbatar da afkuwar lamarin, Kwamishinan Ilimi na jihar, Shehu Muhammad Makarfi ya ce dalibai 450 ne ke kwana da dakunan kwanan biyu.

Ya kuma kara da cewa ba a rasa rai ba sakamakon gobarar.

Ya ce, "Mun gode wa Allah cewa babu dalibar da ta samu rauni ko ta mutu sakamakon gobarar. Har yanzu ba a gano abinda ya yi sanadin gobarar ba amma muna iya kokarin mu domin samar wa daliban katifu da unifom."

Ya kuma yi kira ga iyayen daliban su dawo da yaransu makaranta su cigaba da karatu domin gwamnati ta riga ta dauki matakan ba su masauki a wasu dakunan kwanan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel