'Yan Sanda Sun Hallaka 'Yan Bindiga, Sun Kwato Makamai a Kaduna

'Yan Sanda Sun Hallaka 'Yan Bindiga, Sun Kwato Makamai a Kaduna

  • Jami'an rundunar ƴan sanda a jihar Kaduna sun samu nasarar rage mugun iri bayan sun hallaka miyagun ƴan bindiga mutum biyu
  • Ƴan sandan tare da haɗin gwiwar mafarauta sun sheƙe ƴan bindigan ne bayan sun hallaka wani manomi a gonarsa a ƙauyen Kuriga
  • Bayan yin rangama da ƴan bindigan, tawagar jami'an tsaron ta kuma ƙwato bindigu ƙirar AK-47 guda biyu tare da harsasai 17

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da kashe wasu ƴan bindiga mutum biyu.

Jami'an rundunar ƴan sandan sun kuma ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu a hannun ƴan bindigan masu addabar mutane.

'Yan sanda sun hallaka 'yan bindiga
'Yan sanda sun sheke 'yan bindiga a Kaduna Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Jaridar PM News ta rahoto cewa jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar, Mansir Hassan, ya tabbatar da faruwar lamarin a Kaduna ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

'Mutuwar' wani matashi Kabiru sakamakon azabtarwar ƴan sanda ya tada ƙura a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe aka kashe ƴan bindiga a Kaduna?

Kakakin rundunar ƴan sandan ya bayyana cewa an hallaka ƴan bindigan ne bayan sun hallaka wani manomi a gonarsa a ƙauyen Kuriga a ranar Asabar.

Lamarin ya auku ne a ranar Asabar da misalin ƙarfe 9:00 na safe, bayan wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kashe wani mutum mai suna Isiyaka Mikailu, mai shekara 60 a garin Kuriga, a lokacin da yake gonarsa.

Mansir Hassan ya ce nan da nan aka haɗa tawagar ƴan sandan tafi da gidanka da mafarauta da misalin ƙarfe 12:00 na rana domin zuwa wurin da lamarin ya auku.

"Da isowar tawagar zuwa wurin, sun yi musayar wuta tare da ƴan bindigan."
"A yayin arangamar, an kashe ƴan bindiga biyu, ɗaya mai suna Yusuf daga Rugar Mai Chakun a ƙauyen Kuriga da wani wanda ba a san ko su wanene ba."

Kara karanta wannan

Bayan kashe sojoji, ƴan bindiga sun yi garkuwa da mutane sama da 80 a Katsina

- ASP Mansir Hassan

A cewarsa an samu nasarar ƙwato bindigu ƙirar AK-47 guda biyu da harsasai guda 17, rahoton da tashar Channels tv ta tabbatar.

Ƴan bindiga sun hallaka sojoji

A wani labarin kuma, kun ji cewa an gwabza faɗa tsakanin dakarun sojoji da kuma ƴan bindiga masu biyayya ga Ado Aliero a jihar Katsina.

Lamarin ya yi sanadiyyar mutuwar sojoji biyar da raunata wasu 11 yayin harin da aka kai a sansanin sojoji da ke ƙaramar hukumar Faskari a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel