Wani mutum ya yi barazanar kai coci kotu idan bata biya shi kuɗin baikonsa na shekaru 19 ba

Wani mutum ya yi barazanar kai coci kotu idan bata biya shi kuɗin baikonsa na shekaru 19 ba

- Wani bawan Allah ya ya bukaci coci ta mayar masa da kudin da yawan su yakai KES 58,000

- Ya ce ya bada kudin ne saboda matsawa da tilastawa ba wai don ransa na so ya bayar ba

- Ya yi barazanar zuwa kotu idan aka gaza mayar masa da kudin kafin 31 ga watan Nuwamba

Wani mutum ya rubutawa wata coci bukatar a dawo masa da duk abin da ya bayar a matsayin baiko da sadaka ga cocin tsawon shekara 19.

Dishon Kinyanjui Kinuthia, wani kirista dan Kenya, ya rubata wasikar ta shafin Tuwita ga Cocin kuma ya yi gargadin cewa zai dauki mataki idan ba'a dawo masa da kudadensa ba.

Dishon, wanda ya ke halartar Cocin Revival Mission Church, Kabete, a Nairobi, ya ce ya kasance yana halartar cocin daga shekarar 1997 kafin ya bar cocin a 2018.

Wani mutum ya nemi coci ta mayar masa da baikon da ya yi shekaru 19 yana biya
Wani mutum ya nemi coci ta mayar masa da baikon da ya yi shekaru 19 yana biya. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Yajin aiki: Iyayen ɗalibai za su' ji a jikinsu' idan ba mu yi nasara ba - ASUU

Ya bukaci Cocin da ta mayar masa da kudaden da adadin su yakai KES 58,000 a kudin kenya, wanda shine kiyasinsa na abin da ya kashe wa cocin kusan shekara 20.

Ya ce ya bada gudummawar ne "ba da son ran sa ba" sai saboda "tilastawa, da matsawa da kuma katsalandan."

KU KARANTA: 'Yan shi'a sun ƙona tutar Faransa a Abuja kan kalaman shugaban Faransa, Macron

Ya bukaci cocin ta mayar masa da kudin kafin 31 ga watan Nuwamba, ko kuma ya dauki matakin shari'a.

Wani mutum ya nemi coci ta mayar masa da baikon da ya yi shekaru 19 yana biya
Wani mutum ya nemi coci ta mayar masa da baikon da ya yi shekaru 19 yana biya. Hoto: @lindaikeji
Asali: Twitter

A wani labarin daban, fusatattun matasa a garin Daudu a ƙaramar hukumar Gina, a ranar Talata, sun ƙona Divine Shadow Church kan alaƙanta mai cocin da satar mazakuta a garin kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kwana ki uku da suka shuɗe, matasan sun yi zanga zanga a babban titin Makurdi - Lafia kan abinda suka kira 'batar mazakutar' mutum shida cikin wata guda a garin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel