Matsalar Tsaro: Ministan Tinubu da Tsofaffin Gwamnonin Zamfara Sun Gana a Abuja
- Tsofaffin gwamnoni hudu na jihar Zamfara sun yi taro domin lalubo hanyoyin warware matsalolin tsaro da ke addabar jihar
- Tsofaffin gwamnonin su ne Sanata Ahmed Yarima, Alhaji Mamuda Shinkafi, Sanata Abdulaziz Yari, da kuma Bello Matawalle
- A yayin tattaunawar, tsofaffin gwamnonin sun jaddada ajiye duk wani bambanci na siyasa domin magance matsalar tsaro a Zamfara
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Dangane da tabarbarewar tsaro a jihar Zamfara, wasu tsofaffin gwamnoni hudu na jihar sun yi taro domin lalubo hanyoyin warware matsalolin.
Tsofaffin gwamnonin Zamfara sun gana
Ba iya matsalar tsaro ba, tsofaffin gwamnonin sun gana domin lalubo hanyoyin inganta ci gaban zamantakewa da tattalin arziki, ilimi, da kiwon lafiya a jihar Zamfara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Tribune ta ruwaito tsofaffin gwamnonin sun yi wannan ganawar sirrin a daren ranar Asabar a gidan karamin ministan tsaro, Bello Mohammed Matawalle a Abuja.
Tsofaffin gwamnonion su ne Sanata Ahmed Sani Yarima, Alhaji Mamuda Shinkafi, Sanata Abdulaziz Yari Abubakar, da kuma karamin ministan tsaro, Bello Mohammed Matawalle.
An ajiye bambancin siyasa a gefe
Rahotanni sun ce, tsoffin gwamnonin sun hada kai ne domin tattaunawa kan dabarun tunkarar kalubalen tsaro da Zamfara ke fama da su da kuma inganta rayuwar al’ummar jihar.
Tsofaffin gwamnonin sun jaddada cewa, a tattaunawar da ake yi kan tsaro, dole ne a ajiye duk wani banbanci na siyasa domin amfanin jama’a, in ji rahoton BBC Hausa.
A baya-bayan nan dai 'yan bindiga na ci gaba da kai hare-hare a garuruwan jihar Zamfara, wanda ke zama silar mutuwar wasu da kuma yin garkuwa da dama.
'Yan sandan jihohi: Ina aka kwana?
A wani labarin, mun ruwaito cewa kudurin fadar shugaban kasa, 'yan majalisun tarayya da gwamnoni na kafa 'yan sandan jihohi ya samu goyon bayan shugabannin majalisun jihohi.
A wani zama da kungiyar shugabannin majalisun jihohi 36 suka yi a Abuja, sun amince a samar da rundunar 'yan sandan jihohi domin magance matsalar tsaro a kasar.
Majalisar dattawa da ta wakilai na kokarin yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 1999 domin saka wasu batutuwa kamar dokar kafa ‘yan sandan jihohi.
Asali: Legit.ng