Rikicin Zamfara: Akwai hannun tsofaffin Gwamnoni, ya kamata a tsige Sarakuna 15

Rikicin Zamfara: Akwai hannun tsofaffin Gwamnoni, ya kamata a tsige Sarakuna 15

Halin rashin tsaro ya jefa Bayin Allah rututu a halin ha’ula’i a jihar Zamfara

Binciken da kwamiti ya yi ya nuna inda aka samu matsala daga 1999 - 2019

Ana zargin wasu Gwamnoni da Sarakuna wajen kara huta wutan rigingimun

Zamfara - Wani rahoto da Vanguard ta fitar, ya nuna cewa mutane sama da 6, 300 suka mutu a rikicin Zamfara, sannan an yi garkuwa da mutane 3, 672.

A dalilin rikicin, an maida mata 6,483 zawarawa, yara 25,050 sun zama marayu. An sace shanu 215, 241 da sauran dabbobi 160, 000, an kona gidaje 3, 587.

Jaridar Vanguard tace har yau ba a dabbaka mafi yawan shawarwarin da kwamitin da ya binciki rikicin na Zamfara ya ba gwamnatin Bello Matawalle ba.

Da an yi aiki a kan rahoton da kwamitin ya ba gwamna, da an gurfanar da wani tsohon gwamnan jihar, sannan a tsige wasu daga cikin sarakunan da ke jihar.

Read also

Rahoto: Halin da ake ciki na harin 'yan bindiga duk da katse hanyoyin sadarwa a Zamfara

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Haka zalika da an gurfanar da wasu jami’an sojoji 10 a sakamakon zarginsu da hannu a kashe-kashen.

Binciken da aka gudanar ya nuna daga cikin abubuwan da suka hura wutan rikicin akwai daukar doka a hannu, da raba wa mutane jeji a matsayin filin noma.

Gwamnan Zamfara
Gwamna Bello Muhammad Matawalle Hoto: premiumtimesng.com
Source: UGC

Kuskuren da gwamnoni suka yi

Jami’an sa-kai da aka rika kirkiro wa sun rika kashe wadanda ake zargi da laifi. Wannan ya hada fada tsakanin Fulani da mazauna wasu kauyuka a Zamfara.

A lokacin da ‘yan fashi suka addabi jihar Zamfara, sai gwamnatin Ahmed Sani Yariman Bakura ta share jeji domin rika noma a inda ‘yan fashin ke fake wa.

Wannan matsaya da gwamnan ya dauka ya jawo rigima tsakanin manoman da masu kiwon dabbobi.

Da Mamuda Aliyu Shinkafi ya zama gwamna a 2007, an rika raba wa manyan gwamnati filaye domin su yi noma. Hakan ya kara jawo aka rasa wuraren kiwo.

Read also

Gwamnan Neja ya dakatad da zaben sabon Sarkin Kontagoran kan zargin murdiya

Yari da wasu Kwamishinoninsa

Binciken kwamitin ya nuna gwamnatin Abdulaziz Yari Abubakar ta gaza magance matsalar, ta jawo ‘yan bindiga daga nesa suka rika shigo wa jihar Zamfara.

Wannan ya sa kwamitin ya bada shawarar a kama gwamna Abdul’Aziz Yari Abubakar da wasu hadimansa; Bello Dankande Gamji, da Sani Gwamna Mayanchi.

Kwamitin sun ba gwamna shawarar ya tunbuke rawanin Sarakuna 15 daga cikin Sarakuna 17 da ke jihar Zamfara, saboda zarginsu da ake yi da hada-kai da miyagu.

Source: Legit.ng

Online view pixel