Rigima Ta Kaure Tsakanin Jami'an DSS da Ma'aikata a Zauren Majalisar Tarayya a Abuja
- Rikici ya ɓarke tsakanin wasu jami'an DSS da ma'aikata a zauren majalisar tarayya da ke Abuja ranar Jumu'a
- Lamarin ya faru ne lokacin da jami'an DSS suka hana wasu manyan ma'aikata wucewa har suka fara hayaniya, wanda ya ja hankalin sauran ma'aikata
- Tuni dai DPO na cikin majalisa da mataimakiyar magatakardan majalisar dattawa suka shawo kan lamarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Rahoton da ke shigowa daga Abuja ya nuna cewa an samu wata yar hatsaniya tsakanin jami'an hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) da ma'aikatan majalisa.
Lamarin dai ya faru ne yayin da ka-ce-na-ce ya haɗa jami'an DSS da wasu manyan ma'aikata biyu a ƙofar shiga sashin White House da ke zauren majalisar tarayya (NASS).
Jaridar Leadership ta ce rigimar ta faru ne da misalin ƙarfe 11:45 na safiyar yau Jumu'a a ƙofar da ta raba sabon ginin majalisar dattawa da sashin White House.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meya haddasa rikici a Majalisa?
Rikicin ya fara ne lokacin da jami'an DSS da ke gadin ƙofar suka nemi wasu manyan ma'aikatan NASS biyu su bayar da katinsu na shaida kafin su wuce.
Ganau ya tabbatar da cewa jami'an biyu, John Nnadi mai aiki da kwamitin mai na majalisar dattawa da mataimakin darakta, Chris Odoh, sun nuna wa jami'an katinsu.
A cewarsa duk da sun nuna wa jami'an DSS katin shaidarsu amma suka tsayar da su bisa zargin cewa ba su gabatar da kansu yadda ya kamata ba.
A matsayinsu na manyan ma’aikatan NASS, sun yi yunƙurin shiga ɓangaren White House amma jami’an DSS suka hana su, lamarin da ya haddasa hatsaniya.
An ci zarafin ma'aikatan majalisa
Duk wani yunƙuri da masu wucewa suka yi domin sasanta rikicin bai cimma nasara ba, sai da jami'an DSS suka fara cin mutuncin ma'aikatan, suka wuce da su Ofis.
Yadda jami'an tsaron suka ɗauki mutanen biyu da tsiya zuwa ofishinsu na cikin majalisar, wanda bai wuce nisan mita 125 ba ne ya jawo hankalin sauran ma'aikata.
DPO ya shawo kan lamarin
A fusace ma'aikatan majalisa suka cika ƙofar ofishin DSS kuma suka yi barazanar cewa za su ɗauki tsattsauran mataki matuƙar ba a saki waɗanda aka kama ba, cewar Daily Trust.
Shugaban ƴan sandan majalisa (DPO), Alex Annagu, da mataimakiyar magatakardan majalisar dattawa, Misis Ilobah Isabella, sun hanzarta zuwa wurin domin shawo kan lamarin.
Mutum akalla 15 sun rasu a Kano
A wani rahoton kuma Ƴan sanda sun tabbatar da cewa zuwa yanzu mutum 15 sun mutu sakamakon harin da aka kai masallaci ranar Laraba a Kano.
Kwamishinan ƴan sandan jihar, CP Usaini Gumel ya bayyana cewa ƴan sanda na kan bincike kan lamarin wanda ya auku a kauyen Gadan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng