Niger: Ministar Tinubu Ta Yi Amai Ta Lashe, Ta Dauki Mataki Kan Aurar da Mata 100
- Yayin da ake ta cece-kuce kan aurar da mata marayu a jihar Niger, Minista ta janye karar da ta shigar kan kakakin Majalisa
- Uju Kennedy-Ohanenye ta dauki matakin ne bayan ganawa da Majalisar jihar da kuma sarakunan gargajiya a jihar
- Kennedy-Ohanenye ta ce za su yi bincike kan shekarun yaran domin tabbatar da ko sun kai a aurar da su ko sabanin haka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Ministar harkokin mata, Uju Kennedy-Ohanenye ta janye ƙorafin da ta shigar a kotu kan kakakin Majalisar Niger, Abdulmalik Sarkin-Daji.
Ministar ta dauki matakin ne kan shirin aurar da mata marayu 100 a jihar Niger da Sarkin-Daji ya shirya daukar nauyi.
Musabbabin janye ƙorafin Ministar a Niger
Uju ta bayyana haka ne a yau Juma'a 17 ga watan Mayu inda ta ce sun yi haɗaka da Majalisar jihar da sarakuna a jihar domin gudanar da bincike.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ministar ta ce hakan zai ba su damar gano ainihin shekarun yaran matan da za a aurar domin tabbatar da musu adalci, cewar Channels TV.
Ta ce ma'aikatarta za ta kula da karatu da kuma samarwa yaran sana'o'i da ma sauran marayu da rashin tsaro ya yi ajalin Iyayensu, cewar Leadership.
Ministar ta shigar da kara kan auren
Wannan ya biyo bayan maka kakakin Majalisar jihar, Abdulmalik Sarkin-Daji a kotu kan shirinsa na aurar da mata 100 a karamar hukumar Mariga.
Daga bisani Sarkin-Daji ya janye kudurinsa na daukar nauyin aurar da yaran inda ya ce daman taimako ya yi niyyar yi.
Kotu ta hana auren mata a Niger
A wani labarin, kun ji cewa Babbar Kotun Tarayya ta yi hukunci kan shirin aurar da mata marayu 100 a jihar Niger.
Kotun tarayya ta dakatar da shirye-shiryen gudanar da bikin bayan shigar da kara da Ministar mata, Uju Kennedy-Ohanenye ta yi.
Ministar ta samu iko daga kotun kan duk matakin da ta dauka game da shirin aurar da matan da ake yi a karshen wannan wata.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng