“Dalilin da Ya Sa Dattawan Arewa Ke Nadamar Zaben Tinubu a 2023,” in Ji Tsohon Gwamna

“Dalilin da Ya Sa Dattawan Arewa Ke Nadamar Zaben Tinubu a 2023,” in Ji Tsohon Gwamna

  • Tsohon gwamnan Katsina, Aminu Masari, ya caccaki kungiyar dattawan Arewa (NEF) bisa kalaman da suka yi kan Shugaba Bola Tinubu
  • Aminu Masari ya ce wadanda ke nadamar zaben Tinubu a 2023 suna hankoro ne saboda ba su samu abinda suke so ba a gwamnatin
  • Tsohon gwamnan ya jaddada cewa sun zabi Tinubu saboda cancanta ne, don haka bai kamata a fara adawa da shi a cikin shekara daya ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Tsohon gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari, ya caccaki kungiyar dattawan Arewa (NEF) bisa nuna nadamar goyon bayan Shugaba Bola Tinubu a zaben 2023.

Aminu Masari ya kalubalanci dattawan Arewa
Tsohon gwamnan Katsina ya yi magana kan zaben Tinubu a 2023. Hoto: @GovernorMasari
Asali: Twitter

Aminu Masari ya ce wadanda suka goyi bayan shugaban kasar a 2023 amma yanzu su ke nadama, sun yi biyayya ne tun farko domin biyan bukatarsu ba domin cancantar Tinubu ba.

Kara karanta wannan

'Tinubu ya yi watsi da mu bayan zaben 2023', shugabannin mata na APC sun koka

Dattawan Arewa sun soki gwamnatin Tinubu

Da yake zantawa da jaridar Daily Trust, tsohon gwamnan ya ce bai kamata a fara sukar gwamnatin Tinubu ba daga yin shekara daya a mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan ba a manta ba, a watan jiya ne kungiyar NEF, ta bayyana cewa Arewa ta yi kuskure wajen zaben Bola Tinubu a matsayin shugaban kasa a 2023.

Ta bakin mai magana da yawunta, Abdul-Azeez Suleiman, kungiyar NEF ta ce ba za ta yarda ta tafka irin wannan kuskuren a zabe na gaba ba.

Sanarwar ta haifar da martani daban-daban, inda karamin ministan tsaro, Bello Matawalle ya yi tir da kalaman kungiyar dattawan Arewan.

Tsohon gwamna ya kare gwamnatin Tinubu

A martanin Aminu Masari, ya dage kan cewa Tinubu ya dauki alkawarin janye tallafin man fetur a gaban sauran jiga-jigan 'yan takara a zaben shugaban kasa na 2023.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: EFCC ta na neman gwamnan PDP ruwa a jallo? Gaskiya ta fito

Don haka bai kamata a rika amfani da cika alkawarin da ya yi a matsayin abin da za a soki gwamnatinsa da shi ba duk da cewa jama'a na wahala.

"Wadanda ke nadamar zaben Tinubu dama can sun zabe shi saboda wasu manufofi na su, da suka kasa cimma muradunsu ne yanzu su ke sukar gwamnatin.
"Amma mu mun ga cancanta a tattare da shi, wannan ne ma dalilin da ya sa muka zabe shi. Bai kamata a fara sukar gwamnatinsa ba daga yin shekara daya a mulki."

NELFund: Gwamnati ta aika sako ga dalibai

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta aika muhimmin sako ga daliban Nigeria kan ranar da za su fara neman rancen kudin karatu.

Hukumar kula da asusun ba da lamunin karatun (NELFund) ya sanar da ce zai bude shafin neman bashin daliban a ranar 24 ga watan Mayun 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.