Samar da Tsaro: Shugabannin Majalisu 36 Sun Goyi Bayan Kafa ’Yan Sandan Jihohi

Samar da Tsaro: Shugabannin Majalisu 36 Sun Goyi Bayan Kafa ’Yan Sandan Jihohi

  • A yayin da majalisar dattawa da ta wakilai ke fafutukar kafa 'yan sandan jihohi, shugabannin majalisar jihohi 36 sun goyi baya
  • A ranar Alhamis, 16 ga watan Mayun nan ne shugabannin majalisun suka yi wata ganawa a Abuja tare da bayyana amincewar su
  • Kakakin majalisun 36 da ake da su sun ce kafa ‘yan sandan jihohi zai taimaka wajen magance matsalar rashin tsaro a fadin kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugabannin majalisar jihohin Najeriya 36 sun goyi bayan yunkurin da majalisun dokokin kasar ke ci gaba da yi na samar da ‘yan sandan jihohi.

Shugabannin majalisun jihohi 36 sun gana a Abuja kan 'yan sandan jihohi
Kakakin majalisun jihohi 36 sun goyi bayan kafa 'yan sandan jihohi. Hoto: @PoliceNG
Asali: Twitter

Shugabannin majalisu 36 sun dauki matsaya

Shugabannin sun bayyana kudurin nasu ne a wata sanarwa da suka fitar a karshen taron kakakin majalisun jihohin da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa ta zartar da kudurin kafa hukumar raya jihohin Arewa maso Yamma

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar The Cable ta ruwaito kakakin majalisar jihar Oyo kuma shugaban taron, Rt. Hon. Adebo Ogundoyin ya sanya hannu kan sanarwar.

Kakakin majalisun sun ce kafa ‘yan sandan jihohi zai taimaka wajen magance matsalar rashin tsaro a kasar, in ji rahoton Vanguard.

Majalisar dattawa da ta wakilai na kokarin yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 1999 domin saka wasu batutuwa kamar dokar kafa ‘yan sandan jihohi.

Sufetan 'yan sandan ya yi adawa

A watan da ya gabata, mun ruwaito babban sufeton ‘yan sanda (IGP), Kayode Egbetokun, ya ce Najeriya ba ta “kai matakin” fara amfani da ‘yan sandan jihohi ba.

IGP Egbetokun ya yi ikirarin cewa wasu gwamnoni za su yi amfani da ‘yan sandan domin biyan bukatun siyasa wanda zai haddasa rarrabuwar kawuna.

Kara karanta wannan

Dan majalisar PDP ya nemi Tinubu ya fara tafiye tafiye a mota ko ya hau jirgin haya

Tinubu ya gana da gwamnonin jihohi

Tun da fari, a ranar 15 ga watan Fabrairu ne muka ruwaito gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamiti da zai binciki yadda za a kafa ‘yan sandan jihohi a kasar nan.

Mohammed Idris, ministan yada labarai da wayar da kan jama'a na kasa, ya ce shugaban kasa Bola Tinubu da gwamnoni sun amince da tsare-tsaren da za a bi.

Ministan ya kara da cewa, za a gudanar da tarurruka daban-daban domin sanin yadda rundunar ‘yan sandan za ta rika yin aiki ta hanyar karbar umarni na bai daya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel