Abubuwan da Ya Kamata Ku Sani Game da Rigimar NLC Kan Ƙarin Kudin Wutar Lantarki
A farkon watan Afrilu, Gwamnatin Najeriya ta sanar ɗa ƙara kuɗin wutar lantarki ga ƴan rukunin Band A, waɗanke ke samun hasken wuta na sa'o'i 20 kowace rana.
Mataimakin Shugaban Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC), Musliu Oseni, ne ya bayyana haka a taron manema labarai ranar Laraba, 3 ga watan Afrilu.
Ya ce karin kudin zai sa abokan hulda su biya ₦225 a kowace sa’a, ma'ana ya tashi daga ₦66 watau an samu ƙarin kaso 240%, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
Sai dai wannan ƙarin bai yi wa ƴan kwadagon Najeriya daɗi ba, inda suka nuna adawarsu ƙarara da ƙarin kuɗin wutar lantarkin duk da ba kowa ta shafa ba.
A wannan babin, Legit Hausa ta tattaro muku matakan da kungiyoyin kwadago suka ɗauka da kuma matsayarsu kan ƙarin kuɗin wutar lantarki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kudin wuta: NLC, TUC sun ce fau-fau
A karon farko dai manyan ƙungiyoyin kwadago NLC da TUC, har da ɓangaren kamfanoni masu zaman kansu sun yi watsi da wannan mataki na gwamnatin tarayya.
Sun kuma buƙaci gwamnati ta gaggauta janye wannan kudiri wanda a cewarsu zai durƙusar da masana'antu kuma ya lalata kasuwanci.
Ƴan kwadagon sun bayyana cewa a yanzu babu wani wuri a faɗin Najeriya da ake samun wuta tsawon awanni 20 ba tare da tangarɗa ba.
Ƴan kwadago sun yi zanga-zanga
Makonni bayan haka, ƴan kwadago a Najeriya suka fara zanga-zangar nuna rashin aminta da cire tallafin wutar lantarki wanda gwamnati ta yi.
Kungiyoyin NLC da TUC sun jaddada buƙatar cewa a janye karin kudin duk da ba wata wutar kirki ake samu a ƙasar ba, a cewarsu rashin wuta na kawo naƙasu ga tattalin arziki.
Da yake jawabi a bikin ranar ma’aikata ta duniya da aka gudanar a Abuja ranar 1 ga watan Mayu, shugaban NLC, Joe Ajaero, ya ce ba zai yiwu gwamnati ta ƙara kuɗin wuta ba.
Ya ce bai kamata gwamnatin tarayya ta tsoma baki a harkokin kuɗin wuta ba saboda ɓangaren ya bar hannunta tun tuni.
Shi ma Shugaban TUC, Festus Osifo, ya caccaki matakin, inda ya ce, “Ba zai yiwu a tilasta wa ‘yan Nijeriya su biya karin kudin wutar lantarkin da ba a kawo wa."
Kungiyoyin sun ba da wa'adin mako guda tare da yin barazanar mamaye ofisoshin NERC idan har gwamnati ba ta janye kudirinta na cire tallafin lantarki ba.
NLC, TUC sun rufe kamfanonin wuta
A ranar Litinin da ta wuce 13 ga watan Mayu, ƙungiyoyin kwadago suka fantsama zanga-zanga kan ƙarin kuɗin wuta, inda suka rufe rassan kamfanin rarraba wuta (DisCos) a faɗin ƙasa.
Ƴan kwadagon su tare hedkwatar kamfanin rarraba wutar lantarki ta Ibadan (IBEDC), kamfanin rarraba wutar lantarki ta Jos (JEDC), da kamfanin rarraba wutar lantarki ta Benin (BEDC).
NLC da TUC sun kuma yi zanga-zanga a ofisoshin kamfanin raba wuta na Yola (YEDC) da na Ikeja (IKEDC), da na hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya (ERCN).
Da suke nuna rashin jin dadinsu da karin, ƴan kwadagon ta bukaci a soke wannan karin ga kwastomomin da ke rukunin Band A, The Cable ta rahoto wannan.
Meyasa Gwamnatin Tinubu ta ƙara kuɗin wuta?
Sai dai duk wannan ƙura da ta tashi kan ƙarin kuɗin, ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya kare gwamnatin tarayya, ya ce duk da haka za a biya tallafi a 2024.
Adelabu ya bayyana cewa gwamnati za ta lale N1.8trn a matsayin kuɗin tallafin wutar lantarkin da ƴan Najeriya za su sha a 2024.
Ya kuma ƙara da cewa gwamnati na da hujjar ƙara kuɗin wutar domin kundin dokar samar da wuta 2023 ya tanadi cewa za a iya ƙara kuɗin wuta sau biyu a shekara.
A cikin shirin siyasa a yau na gidan talabijin Channels, Adelabu ya ce:
"Doka ta halatta wa hukumar NERC sake nazarin kuɗin wutar lantarki, ta ba hukumar damar haka sau biyu a shekara, watau duk bayan watanni shida."
Ƴan Najeriya sun mayar da martani
Duk da mafi yawa ƙarin kuɗin bai shafe su ba amma ƴan Najeriya sun nuna fushin su da cewa ƙarin ya gangaro har zuwa kansu.
Usman Bandiro, wani ɗan karamar hukumar Ɗanja a jihar Katsina, ya shaidawa Legit Hausa cewa ƴan NEPA sun ƙara yawan kuɗin da suke amsa duk wata ba tare da wani dalili ba.
"Gwamnati ta ce ƴan Band A kaɗai aka kara wa kuɗi amma mu da ko mita bamu da ita an ƙara mana kuɗi, ya kamata a ɗauki mataki domin komai dai kan talaka yake ƙarewa."
A nasa hangen, Aliyu Yusuf, wani makanike a Katsina, ya ce shi ya dawo daga rakiyar gwamnati a Najeriya domin ya daina sa ran za ta yi wani abu don talaka.
Abubakar Sulaiman, wani mai sana'ar caji ya bayyana cewa a ƴan makonnin nan suna samun wuta sosai a Dabai da ake jihar Katsina amma kwana biyu an daina kawo wa.
Ya ce bai kamata a ƙara kuɗin wuta a irin wannan lokacin da kowa ke shan wahala ba, matuƙar da gaske saboda talaka suke yi.
Tinubu ya fara biyan bashin wuta
A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya ba da umarnin biyan bashin kuɗaɗen da ake bin ɓangaren wutar lantarki wanda ya haura N3.3trn.
Shugaban ƙasar ya amince a biya bashin a hankali a hankali domin magance matsalar rashin samun wutar lantarki a ƙasar nan.
Asali: Legit.ng