Hukumar FIRS Ta Tara Naira Tiriliyan 3.94 a Watanni 3, Ta Fadi Biliyoyin da Take Hari a 2024
- Daga farkon watan Janairu zuwa karshen watan Maris, hukumar FIRS ta bayyana cewa ta tara Naira tiriliyan 3.94 na kudin haraji
- Shugaban FIRS, Zacch Adedeji ne ya bayyana adadin kudin a ranar Alhamis inda ya ce suna son tara Naira tiriliyan 19.4 a 2024
- Mista Adedeji ya bayyana haka ne a yayin da shugabannin hukumar CRMI suka kai ziyara zuwa hedikwatar FIRS da ke Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar tara haraji ta kasa FIRS ta ce ta tara kudaden haraji na Naira tiriliyan 3.94 a cikin watanni uku na farkon shekarar 2024 (Q1).
Shugaban hukumar FIRS, Zacch Adedeji ne ya bayyana adadin kudaden a ranar 15 ga watan Mayun 2024.
FIRS ta gaza tara N4.8trn a wata 3
Jaridar The Cable ta ruwaito kudin ya yi kasa da Naira Tiriliyan 4.8 da hukumar ta sa ran tarawa a duk bayan watanni uku har shekarar ta kare.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Adedeji ya bayyana haka ne a yayin wata ziyarar ban girma da shugabannin hukumar CRMI, karkashin jagorancin Ezekiel Oseni, suka kai hedkwatar FIRS da ke Abuja.
Ya ce kudin da aka tara a farkon 2024 ya zarce wanda aka samu a farkon 2023 da kashi 56.7, kamar yadda rahoton Arise TV ya nuna.
'Ana burin tara N19.4trn a 2024' - FIRS
Musta Adedeji wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan hukumarsa, Mista Tayo Koleosho a wajen taron, ya ce yana da burin tara Naira tiriliyan 19.4 a shekarar 2024.
A cewar Adedeji:
“A cikin shekarun da suka gabata karkashin gwamnatoci daban-daban, hukumar FIRS ta kasance ta na gudanar da ayyukanta na tara kudaden shiga tare da cimma muradin gwamnati."
Dalla-dalla: Albashin 'yan majalisar Nigeria
A wani labarin, mun ruwaito cewa majalisar dattawa, wakilai da ta jihohi 36 tare da hukumomin da ke karkashin su za su kashe kimanin N720bn a 2024.
Wannan kudin ya shafi albashin 'yan majalisar da alawus dinsu da kuma na ma'aikatan da ke karkashin su kamar yadda muka yi bayani dalla-dalla kan yadda za a kashe kudin.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng