Abia: Birkin Tirela ya Shanye, Mota ta Murkushe Mutane 18 a Shingen 'yan Sanda

Abia: Birkin Tirela ya Shanye, Mota ta Murkushe Mutane 18 a Shingen 'yan Sanda

  • Ana fargabar mutane 18 sun rasa ransu a yayin da babbar mota ta bi ta kan motar da su ke ciki a shingen ‘yan sanda
  • Rahotanni sun ce wani dan sanda ne ya tare motar fasinjojin a lokacin da babbar motar ta kwace, ta kuma murje su
  • A halin yanzu dai direbobi sun rufe hanyar tare da yin zanga zanga domin nuna rashin jin dadinsu kan kashe mutanen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Abia - Akalla mutane 18 ne su ka mutu a babban titin Port Harcour zuwa Enugu da ke yankin Umuahia-Enugu a jihar Abia a safiyar yau Alhamis.

Kara karanta wannan

Ana tsoron rikici kan tukunyar miya ya jawo asarar rayuka a birnin Abuja

Rahotanni sun bayyana cewa wata babbar mota ta bi ta kan motar mai daukar fasinjoji 18 a dai-dai shingen ‘yan sanda da ke Lokpanta a jihar.

Accident
Babbar mota ta take mutane 18 Abia (An saka hoton ne domin misali) Hoto: Pius Utomi Ekpei
Asali: Getty Images

The Nation ta wallafa cewa motar na tsaye ta na jiran ‘yan sanda su kammala duba su, sai babbar motar ta kwace.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tirela ta bi ta kan fasinjoji

A safiyar yau Alhamis ne direban wata babbar mota ya bi ta kan fasinjoji 18 yayin da su ke tsaye su na jiran ‘yan sanda su duba su.

Wani shaidar gani da ido, Mista Banana Okereke ya bayyana cewa gawarwakin mutanen da aka take sun watsu a kan titi, yayin da mutane su ka shiga wani hali.

Pulse Nigeria ta tattaro cewa yanzu haka wasu mutane, ciki har da abokan direban motar sun rufe hanya su na neman a bi musu hakkinsu.

Kara karanta wannan

Majalisa ta amince gwamnati ta karbo bashin $500m a magance matsalar wuta

A kalamansa:

“Direbobin motoci sun rufe hanyar su na neman a dawo da dan sandan da ya tare hanya har aka samu mummunan hatsarin.”

Mota ta yi ajalin yarinya a Lagos

Mun kawo mu ku labarin yadda mota ta take wata yarinya mai shekaru biyar, Bosede a titin Iganmu zuwa Apapa da ke jihar Lagos, wanda ya yi sanadiyyar rasuwarta.

Lamarin ya jefa mutane cikin jimami yayin da jami’in hulda da jama’a na jihar, SP Benjamin Hundeyin, ya bayyana cewa an shiga farautar direban.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.