Gwamnati Ta Kama Baburan ’Yan Acaba 220 Yayin da Za a Rusa Gidaje 500 a Lagos

Gwamnati Ta Kama Baburan ’Yan Acaba 220 Yayin da Za a Rusa Gidaje 500 a Lagos

  • Gwamnatin jihar Lagos ta kafa kwamitin kar ta kwana domin rushe daruruwan gine-ginen da aka yi ba bisa ka’ida ba a yankin Lekki
  • Kwamitin, karkashin jagorancin CSP Shola Jejeloye da zai yi aikin na ganin rushe gidajen zai taimaka wajen rage ayyukan bata gari
  • CSP Jejeloye ya ce sun kama babura 220 da suka karya doka wajen bin wasu hanyoyi a biranen jihar da aka haramta babura su bi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Lagos-Hukumomi a jihar Lagos sun dauki gagarumin aikin tsaftace gine-ginen da aka yi ba bisa ka’ida ba a yankin Lekki.

Kwamitin kar-ta-kwana da Gwamnatin jihar ta kafa domin gudanar da aikin karkashin jagorancin CSP Shola Jejeloye zai rushe dakunan da aka gina a yankin.

Kara karanta wannan

Shugaban APC Ganduje zai sarara bayan kotu ta dakatar da bincikensa

Gwamnan jihar Lagos
Gwamnati za ta fara rusau a jihar Lagos Hoto: Babajide Sanwo-Olu
Asali: Facebook

CSP Shola Jejeloye ya bayyana cewa idan an rushe daruruwan gine-ginen, ana sa ran zai taimaka wajen kakkabe ayyukan bata-gari a yankin, kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama babura a birnin Lagos

Shugaban kwamitin kar-ta-kwana, CSP Shola Jejeloye ya bayyana cewa sun kama wasu masu babura da ke bin titunan Victoria Island, da Bourdillon.

Haka zalika baburan suna bin hanyoyin Falomo, da Ikeja, da Abeokuta Expressway, da Ojodu Berger, da Fagba, duk da hana su da gwamnati ta yi.

Ya ce an kama baburan haya guda 220, kuma za su ci gaba da tilasta cewa matuka baburan har sai an bi dokar gwamnati, kamar yadda Punch News ta wallafa.

CSP Shola Jejeloye ya gargadi matuka baburan da su guji karya dokar gwamnati domin tsaftace hanyoyin da ke jihar Lagos.

Kara karanta wannan

"Tsohon gwamna Nyesom Wike ya tarawa Ribas Bashi," Simi Fubara ya fasa kwai

An fara rusau a Ibadan

A baya mun ba ku labarin cewa gwamnatin jihar Oyo ta fara rusau a yankuna daban daban na jihar, kuma ana sa ran gidajen da za a rushe za su kai guda 500.

Da ya ke karin bayan ikan rusau din, kwamishinan filaye, gidaje da raya karkara, Williams Akinfunmilayo ya ce gwamnati za ta biya diyyar dukkanin gidajen da aka rushe.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel