"Abin da Ya Sa Na Ƙona Mutane Suna Sallah a Kano," Wanda Ake Zargi Ya Faɗi Gaskiya

"Abin da Ya Sa Na Ƙona Mutane Suna Sallah a Kano," Wanda Ake Zargi Ya Faɗi Gaskiya

  • Shafi'u Abubakar, wanda ake zargi da ƙona mutane a Masallaci a Kano ya bayyana gaskiyar abin da ya sa ya ɗauki matakin
  • Kakakin ƴan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce wanda ake zargin ya faɗa masu cewa ya ƙona masallatan ne saboda an zalunce shi a rabon gado
  • A halin yanzu ƴan sanda na ci gaba da bincike kan lamarin wanda ya bar aƙalla mutum 24 kwance a asibiti suna jinya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Da safiyar yau Laraba ne aka tashi da labarin ƙona mutane suna tsaka da Sallah a wani masallaci a Laraba Abasawa, ƙaramar hukumar Gezawa a Kano.

Tuni dai rundunar ƴan sandan jihar Kano ta tabbatar da kama wanda ake zargi da bankawa masallacin wuta mai suna Shafi’u Abubakar, ɗan kimanin shekara 38 a duniya.

Kara karanta wannan

Kotun Ingila ta yanke wa ɗan Najeriya hukunci bisa laifin kashe matarsa

Kwamishinan ƴan sandan Kano, Usaini Gumel.
Shafi'u Abubakar ya faɗi dalilinsa na ƙona masallaci a Kano Hoto: Kano Police Command
Asali: Twitter

Mutum 24 daga cikin masallata 40 da ke cikin masallacin sun samu raunin ƙuna a wurare daban-daban, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zuwa yanzu dai an garzaya da waɗanda aka ceto zuwa asibitin Murtala Muhammad da ke cikin birnin Kano domin a yi masu magani.

Meyasa Shafi'u ya ƙona masallata a Kano?

Mai magana da yawun rundunar ƴan sanda, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da cewa wanda ya aikata ɗanyen aikin na tsare a hannun ƴan sanda.

A wata sanarwa da ya fitar, Kiyawa ya bayyana cewa Shafi'u ya miƙa kansa ga ƴan sanda bayan ya bankawa masallacin wuta.

Wanda ake zargin, Shafi'u ya faɗawa ƴan sanda cewa ya yi haka ne cikin fushi kuma domin ya ɗauki mataki kan waɗanda yake ganin sun zalunce shi a rabon gadon gidansu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun tarwatsa ƙauyuka 50, sun sace mutane sama da 500 a Arewa

Ya ce dukkan waɗanda yake zargin da hannunsu aka cuce shi a rabon gadon suna cikin masallacin a lokacin da ya cinna wutar, cewar The Nation.

Ƴan sandan jihar Kano na kan bincike

Kakakin ƴan sandan ya ce:

"Mun gano wanda ya aikata laifin kuma yanzu haka ya shiga hannun ƴan sanda, sunansa Shafi'u Abubakar, ɗan shekara 38 a duniya.
"Ya faɗa mana cewa yana sane ya ƙona masallacin saboda wani saɓani kan rabon gado kuma duk waɗanda yake tunanim sun zalunce shi suna cikin masallacin a lokacin."
"Shafi'u ya ce ya ɗauki wannam matakin ne domin nuna fushinsa kan lamarin rabon gadon. A yanzu dai wanda ake zargin yana hannun ƴan sanda kuma za a ci gaba da bincike."

An dakatar da wani likita a Kano

A wani rahoton Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da wata likita mai wankin koda a asibitin koyarwa na Muhammad Abdullahi Wase da aka fi sani da asibitin Nassarawa.

Kara karanta wannan

Rikicin shugabancin daba: Mutum 3 sun mutu yayin da wani faɗa ya ɓarke a Kano

Shugaban hukumar kula da manyan asibitocin Kano, Dr. Mansur Mudi Nagoda ne ya bayyana dakatar da likitar saboda kin zuwa wanke kodar wani mara lafiya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262