Emefiele: Tsohon Gwamnan CBN Ya Fara Girbar Abin da Ya Shuka Wajen Canjin Kuɗi

Emefiele: Tsohon Gwamnan CBN Ya Fara Girbar Abin da Ya Shuka Wajen Canjin Kuɗi

  • Kotu ta bayar da belin tsohon gwamnan CBN Godwin Emefiele kan N300m bayan gurfanar da shi kan sababbin tuhume-tuhume
  • Hukumar EFCC ta sake maida Emefiele gaban kotu kan zargin kashe N18.96bn wajen buga N684.5m na sababbin takardun Naira
  • Sai dai tsohon gwamnan ya musanta aikata laifin da ake tuhumarsa kuma kotu ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 28 ga watan Mayu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta ba da belin tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele kan kudi N300m.

Kotun ta amince da belin Emefiele ne bayan gurfanar da shi a gabanta kan tuhume-tuhume shida da suka shafi buga sababbin takardun Naira ba bisa ƙa'ida ba.

Kara karanta wannan

EFCC: Kotu ta bada belin Emefiele bayan ya ki amincewa da laifi

Godwin Emefiele.
Tsohon gwamnan CBN ya samu beli kan N300m a babbar kotun tarayya Hoto: Mr. Godwin Emefiele
Asali: Facebook

Tsohon gwamnan CBN shi ne kaɗai wanda ake tuhuma a ƙarar wadda ke gaban mai shari'a Maryanne Anenih a babbar kotun tarayya da ke Maitama, The Nation ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Emefiele ya musanta tuhumar da ake masa

Emefiele ya musanta laifin da ake tuhumarsa da su wanda hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta shigar kuma aka karanta a zaman kotun.

Sauran sharuddan belin sun hada da cewa ya gabatar da mutum biyu da za su tsaya masa wadanda kowannensu ya mallaki kadarori a yankin Maitama a Abuja.

Mai shari’a Anenih ta umarci wanda ake kara da ya miƙa takardun tafiye-tafiyensa ga kotu kuma kada ya sa ƙafa ya fita kasar nan ba tare da izinin kotu ba.

Sharuɗɗan belin Godwin Emefiele

Alkaliyar ta amince da sharuddan beli makamancin wannan wanda mai shari’a Hamza Muazu, wani alkalin babbar kotun Abuja, ya gindaya wa Emefiele lokacin da aka gurfanar da shi a gabansa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu na tunanin kwashe kuɗin ƴan fansho ta yi wasu muhimman ayyuka

Mai shari’a Anenih ta buƙaci Emefiele ya miƙa takardun shari'a (CTCs) na takardun da ya mika domin cika belin da mai shari’a Muazu ya bayar a baya.

Daga nan kuma sai ta ɗage zaman zuwa ranar 28 ga watan Mayu, 2024 domin shiga cikin shari'ar gadan-gadan, kamar yadda Channels tv ta rahoto.

DSS ta kai samame harabar kotu

A wani rahoton kun ji cewa jami'an DSS sun kutsa kai cikin kotu ana cikin shari'a, sun tafi da mutum biyu da ake tuhuma a jihar Ogun ranar Talata.

Lamarin dai wanda ya keta doka ya haifar da hayaniya a harabar kotun, inda lauyan waɗanda ake tuhuma ya caccaki DSS.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel