An Gano 'Kuskure' a Tsarin Mulkin Najeriya, Obasanjo Ya Yi Karin Haske

An Gano 'Kuskure' a Tsarin Mulkin Najeriya, Obasanjo Ya Yi Karin Haske

  • Wasu yan majalisar dokokin Najeriya sun fara yunkurin kawo sauyi a tsarin mulkin da ake bi a tarayyar Najeriya
  • Yan majalisar sun kai ziyara ga Obasanjo domin neman goyon baya kan sabon aikin da suka dauka na canja tsarin mulkin
  • Obasanjo ya karbi korafin yan majalisar ya kuma lissafa musu abubuwan da ya kamata su mayar da hankali a kai yayin aikin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Tsohon shugaban kasan Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya ce akwai kurakurai a cikin tsarin mulkin Najeriya.

Obasanjo
Obsanjo ya yi kira kan canja tsarin mulkin Najeriya. Hoto: Pius Utomi Ekpei.
Asali: Getty Images

Tsohon shugaban kasan ya kara da cewa kuskuren ya shafi ƙasashen Afirka da dama da suka yi koyi da Turawan yamma wajen gina tsarin mulki.

Kara karanta wannan

Kayayyaki za su kara tsada a Najeriya, an kara harajin shigo da kayan kasar waje

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa Obasanjo ya magantu ne yayin zantawa da 'yan majalisar tarayya da ke neman canja tsarin mulkin Najeriya.m ko

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yunkurin canja tsarin mulkin Najeriya

Wasu yan majalisar dokokin sun fara yunkurin neman canja tsarin mulkin Najeriya wurin neman goyon bayan manyan kasa.

Yan majalisar wadanda shugaban marasa rinjaye, Kingsley Chinda ke jagoranta sun kai ziyara ga Obasanjo ne domin karin goyon baya kan kudirin nasu.

Wane tsari yan majalisar ke so?

Yan majalisar suna kira ne da a dawo da tsarin mulkin jamhuriya ta farko wanda Obasanjo ya rusa a shekarar 1979.

Tsarin zai ba jam'iyya mai rinjayen ƴan majalisar tarayya rike madafun iko da kuma nada firaminista.

Martanin Obasanjo

Tsohon shugaban kasar ya goyi bayan ƴan majalisar kan kudurin nasu inda ya ce an riga an yi kuskure a baya.

Kara karanta wannan

Jami’an Birtaniya sun yi watsi da Yarima Harry a ziyarar da ya kawo zuwa Najeriya

Ya kuma kara da cewa tsarin mulkin Amurka da Najeriya da wasu kashen Africa suka aro ya sabawa rayuwar Afirka.

Sai dai Obasanjo ya gargadi ƴan majalisar da yin taka tsan-tsan wajen cimma kudirin nasu, cewar rahoton the Cable.

Ya kuma kara da cewa lalle ya kamata su kara duba yiwuwar samar da tsari mafi dacewa da rayuwar ƴan Najeriya.

Obasanjo ya yi kira ga yan Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa Olusegun Obasanjo wanda ya shugabanci Najeriya a lokacin mulkin soja da na farar hula, ya yi kira ga al'umma ƙasar nan.

Tsohon shugaban ƙasar ya buƙaci ƴan Najeriya da kada su yanke ƙauna da ƙasar nan duk da halin kuncin rayuwa da wahalhalu da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng