EFCC ta ayyana neman Akanta Janar da wasu manyan Jami'an gwamnati ruwa a jallo kan N435bn

EFCC ta ayyana neman Akanta Janar da wasu manyan Jami'an gwamnati ruwa a jallo kan N435bn

  • Hukumar yaƙi da cin hanci EFCC ta ayyana neman Akanta Janar na jihar Ribas da wasu mutane kan ɓatan wasu kudi kimanin biliyan N435bn
  • Hukumar ta yi kira ga yan Najeriya da su taimaka mata da sahihan bayanai wajen cafke waɗan da ake zargi
  • Kakakin hukumar ya ce duk wanda ke da wani bayani ya tuntubi kowane ofishi da ke kusa ko wata hukumar tsaro

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta'annadi (EFCC) ta ayyana neman Akanta Janar na jihar Ribas, Fubara Siminayi, da wasu mutum 58 kan zargin ɓatan biliyan N435bn.

Hukumar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar ranar Talata kuma jaridar Punch ta gani.

EFCC na neman Akanta Janar na Ribas.
EFCC ta ayyana neman Akanta Janar da wasu manyan Jami'an gwamnati ruwa a jallo kan N435bn Hoto: punchng.com
Asali: UGC

EFCC na neman Siminayi da wasu manyan jami'an gwamnatin jihar Ribas guda hudu da sauran su bisa tuhume-tuhume kan wasu makudan kudi da suka yi ɓatan dabo biliyan N117bn.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun yi ajalin mahaifiya da 'ya'yanta hudu, sun haɗa da wasu mutum biyu

Daga cikin zargin da EFCC take wa mutanen sun haɗa da zamba cikin aminci, haɗa baki, halasta kudin haram, karkatar da kudin al'umma da kuma cin mutuncin Ofis.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jami'i mai hulɗa da jama'a na hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, ya yi kira ga yan Najeriya su taimaka da bayanai don samun nasarar damƙe Akanta Janar da sauran waɗan da ake zargi.

A kalamansa Uwujaren ya ce:

"Muna kira ga duk wani mutumi da yake da wasu sahihan bayanai kan inda Akanta Janar din ya shiga da ya tuntuɓi Ofishin mu ma fi kusa da shi ko caji Ofis ɗin yan sanda ko wata hukumar tsaro ma fi kusa da shi."

Jami'an EFCC sun yi wa gidan Okorocha kawanya

A wani labarin kuma Jami'an EFCC sun mamaye gidan ɗan takarar shugaban kasa a APC zasu kama shi a Abuja

Kara karanta wannan

Cikin katatafaren kadarorin da suka tsunduma AGF Ahmed Idris a komar EFCC

Dakarun EFCC sun yi dirar mikiya a gidan tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha da ke birnin tarayya Abuja.

Rahoto ya nuna cewa jami'an EFCC sun manaye gidan ta ko ina, sun nemi a ya miƙa kansa ko kuma ya amsa gayyata zuwa ofishin su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel