Ministar Tinubu Ta Maka Kakakin Majalisa a Kotu Kan Shirin Aurar da Mata Marayu 100

Ministar Tinubu Ta Maka Kakakin Majalisa a Kotu Kan Shirin Aurar da Mata Marayu 100

  • Ministar mata, Uku Kennedy-Ohanenye ta fusata kan shirin kakakin Majalisar jihar Niger na aurar da yaran mata marayu
  • Kakakin Majalisar, Abdulmalik Sarkin-Daji ya sanar da ɗaukar nauyin auren yaran mata marayu guda 100 a mazabarsa
  • Bayan matakin da Ministar ta dauka, Sarkin-Daji ya dakatar da shirin gudanar da bikin yaran inda ya ce daman daukar nauyi zai yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Ministar mata a Najeriya, Uju Kennedy-Ohanenye ta maka kakakin Majalisar jihar Niger kan shirin aurar da mata 100.

Ministar ta dauki matakin ne domin kalubalantar kakakin Majalisar, Abdulmalik Sarkin-Daji kan shirin aurar da yaran marayu mata 100 a jihar.

Kara karanta wannan

Ministar Tinubu ta jawo an fasa ɗaura auren marayun ƴan mata 100 a jihar Niger

Minstar Tinubu ta fusata kan shirin kakakin Majalisa na aurar da mata 100
Ministar mata, Uju Kennedy-Ohanenye ta maka kakakin Majalisar Niger a kotu kan shirin aurar da mata marayu 100. Hoto: Uku Kennedy-Ohanenye, Abdulmalik Sarkin-Daji.
Asali: Facebook

Minista ta fusata kan aurar da mata

Kennedy-Ohanenye ta bayyana haka ne a Abuja a jiya Litinin 13 ga watan Mayu yayin ganawa da manema labarai, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, Ministar ta tura takarda ga Sufetan 'yan sanda, Kayode Egbetokun kan dakile wannan shiri na kakakin Majalisar, cewar rahoton Leadership.

Kennedy-Ohanenye ta ce an kaddamar da kwakkwaran bincike kan daurin auren da aka saka a ranar 24 ga watan Mayu.

Ta ce wannan mataki bai dace ba, ya kamata a duba yadda za a inganta rayuwar yaran ne a nan gaba.

Hari ila yau, Ministar ta yi alkawarin cewa ma'aikatarta za ta dauki nauyin karatun yaran da kuma sana'o'insu.

Kakakin Majalisar ya dauki mataki

Daga bisani, Kakakin Majalisar jihar Neja, Abdulamlik Sarkindaji ya dakatar da shirin ɗaukar nauyin auren ‘yan mata marayu 100 a mazabarsa.

Kara karanta wannan

Kaduna: Sojoji sun yi ajalin kasurgumin ɗan bindiga, Bangaje da wasu hatsabibai 3

Kakakin majalisar ya bayyana cewa ya fasa aurar da matan saboda abubuwan da suka biyo bayan kudirinsa na taimako.

Sarkindaji ya dauki wannan matakin ne biyo bayan matakin da Ministar mata, Uju Ohanenye ta dauka na kai shi ƙara gaban kotu.

Kakakin Majalisar Niger zai aurar da marayu

Kun ji cewa kakakin Majalisar jihar Niger, Abdulmalik Sarkin-Daji ya shirya aurar da yaran mata marayu guda 100 a mazabarsa.

Kakakin Majalisar ya ce yaran na daga cikin wadanda aka hallaka iyayensu saboda hare-haren 'yan bindiga a jihar a baya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.