Bayan Shekaru 5 da Kashe Shugaban ISWAP Na Farko, Ɗansa Ya Mika Wuya a Maiduguri
- Bayan akalla shekara biyar da kashe Mamman Nur, wanda ya kafa kungiyar ta'addanci ta ISWAP, ɗansa ya mika wuya a Maiduguri
- Mahmud Mamman Nur Albarnawy, ya mika wuya ne a ranar Lahadi, 12 ga watan Mayu ga hukumar tsaro ta NSCDC a karshen mako
- An ruwaito cewa an mika Mahmud zuwa ga cibiyar gyaran tarbiya da tsaftace tunanin mutane ta Bulunkutu domin kara tattara bayanai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Maiduguri, jihar Borno - Babban dan Mamman Nur, wanda ya kafa kungiyar ta'addanci ta ISWAP, Mahmud Mamman Nur Albarnawy, ya mika kansa ga jami’an hukumar NSCDC.
Mahmud, mai shekaru 22, ya mika wuya ne a ranar Lahadi, 12 ga watan Mayu a garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Mahmud Mamman Nur ya mika wuya
Wata majiyar leken asiri ta shaidawa Zagazola Makama cewa binciken hukumar NSCDC ne ya tabbatar da cewa Mahmud Mamman Nur Albarnawy ne babban dan Mamman Nur.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyar ta ce jami’an rundunar sun karbi Mahmud ne ta hannun kawunsa da ke Gamborun Ngala bayan samun labarin cewa yana son mika wuya ga gwamnatin Najeriya a hukumance.
An aika wani amintaccen jami'i domin ya kai shi Maiduguri, kuma an ce sun isa birnin a ranar 11 ga watan Mayu da misalin karfe 1 na rana.
Daga bisani wani jami’in leken asiri na rundunar ya yi wa Mahmud tambayoyi wanda ya bayyana cewa ya tsere daga sansanin Ali Ngulde da ke tsaunin Mandara zuwa Maiduguri.
Yadda Mahmud Nur ya tsere daga Mandara
Mahmud Nur ya ce ya zauna a Gwange da ke babban birnin jihar kafin ya koma Gamboru Ngala ba tare da wata fargaba ko alamun damuwa daga mazauna yankin ba.
A lokacin da yake zaune a Gamboru Ngala, Mahmud ya ce wasu daga cikin masu biyayya ga mahaifinsa sun lallabashi a kan ya koma yankin tafkin Chadi domin yin mubaya’a ga kungiyar ISWAP, amma ya ki yarda.
Ya amsa laifin kai hare-hare a Bama, Banki, Gwoza da wasu wurare da dama a matsayinsa na matsakaitan mayaki a karkashin kungiyar Boko Haram.
An mika Mahmud zuwa ga cibiyar gyaran tarbiya da tsaftace tunanin mutane ta Bulunkutu domin ci gaba da sa ido da tattara bayanai a kansa.
Dan ta'addan Boko Haram ya mika wuya
A wani labarin, mun ruwaito cewa, wani dan ta'addan Boko Haram, Alhaji Wosai ya mika wuya ga sojojin Najeriya na Operation Hadin Kai.
An ruwaito cewa Alhaji Wosai ya mika wuya ne a ranar 11 ga Mayun 2024, bayan ya tserewa daga maboyar ‘yan ta’addan da ke a kauyen Garno da ke jihar Borno.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng