Daga Sambisa: Yadda 'yan Boko Haram suka kashe ogansu Kwamanda Mamman Nur
- Kungiyar 'yan Boko haram sun hallaka daya daga cikin shugabansu
- Kwamanda Nur Wanda ake tunanin ya samu horo daga kungiyar Alqaeda da kuma Al shabab ta Somalia
- Watanni uku da suka gabata mabiyanshi suka hallaka shi abun da yayiwa jami'an tsarin Nigeria dadi matuka
Watannin baya ne, rahotanni suka nuna mayakan Boko Haram, bangaren su Al-BArnawi, sun kashe wani babban Kwamandansu, mai suna Mamman Nur, wanda tuni an tabbatar yayi wa soji da Najeriya ta'asa sosai a baya.
An dai yi ittifakin cewa, mabiya ne suka kashe shi, kuma ga alama, ogansa Habib Albarnawi, wanda tare suka yi wa Sheqau tawaye suka gudu daga Sambisa, shi ya bada odar a hallaka shi.
Batun dai da ya hado su fada, shine Ghanima ta kudin fansar 'yan matan Dapchi da aka basu, inda labaran cikin gida suka ce Al- Barnawi bai ji dadin yadda Mamman Nur ya raba kudin ba, wanda tsakaninsu an kasa gane waye shugaba,
Shi dai Mamman Nur babban Kwamanda ne, wanda ya goge a fagen daga, shi kuwa Habib, kawai tutiya yake cewa shi gadon Boko Haram din yayi daga Uba nai Muhammadu Yusuf.
Su kuwa ISIS sai suka dauki mulki suka baiwa Albarnawy, duk da cewa Mamman Nur yafi shi karfi da salon iya yaki. Sai dai wannan bai hana yaransa dirka masa dalma ba, wanda hakan kuma ya aika tsoro tsakanin manyan mayakan, cewa karshe dai duk manyansu na ta mutuwa ta hannun yara masu zafin kai.
Alamomi dai na nuni da cewa kisan Nur ba abu ne na yin murna ba, face wata alama dake nuni da cewa Boko haram din ta kara hatsari bayan kaurin suna da tayi wajen yin garkuwa da 'yan mata da kananan yara.
Ana dai ganin cewa Mamman Nur yafi shugaban Boko haram Abubakar shekaru saukin kai, wanda shi a bayyane yake nuna cewa su sukasace 'yanmatan Chibok. Lamari da yake alakanta wa da umarnin ubangiji, wai na jihadi da bautar wa, da kama mutane a sayar ko a bautar.
DUBA WANNAN: Bayan bankuna sun shaqe bilyan 7 na daloli a 2010, yanzu Buhari yace dole su dawo dasu lalitar gwamnati
A tsarin Nur harin sa kawai akan sojoji ya tsaya, sannan baya amfani da kananan yara wajen kunar bakin wake. Don haka mutuwarsa wata alama ce dake nuni da cewa, lallai masu zafin ra'ayi sun fi masu sauki daga cikinsu.
Ra'ayin Abubakar Shekau ya saba wa na Nur wanda hakan yasa shekaru suka shude basa ga-maciji da juna, inda Shekau yace Mamman Nur din, ya saba wa dokar Allah, saboda ya fara neman azo ayi sulhu da sojin Najeriya.
Dalilin haka ne yasa Nur da Abu musab Al barnawi wanda da ne ga wanda ya kafa Boko haram suka ware kansu ta hanyar hadewa da kungiyar ta'adanci ta ISIS, dake Iraqi da Syria wadda ita ma tace tsarin Shekau yana da tsauri.
Sun cigaba da gudanar da tsarin ta'adancin su daban da na 'yan Boko haram. Inda Boko Haram tayi zaman ta a Sambisa da kewaye, a kudancin Borno, su kuma suka nausa yankin tafkin Chadi da kasashen Nijar, Kamaru da Chadi, wadanda ke Arewacin jihar Borno.
Boko Haram dai, ta ginu kan wata tatsuniya ne, ta cewa koma me suka yi, wai akwai wani lambu da idan sun mutu zasu je, su sadu da wasu kyawawan mata suyi ta jima'i dasu, zasu kuma ci naman kaza, da giya, da gadaje masu tashi, da kuma lambuna masu inuwa. A kan haka suke wannan kashe-kashen.
Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng
Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng