'Ba zan Sake Rabawa Kowa Tallafin Abinci ba, Kowa ya Koma Noma', Gwamnan Gombe
- Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya ce gwamnatinsa ta rufe kofar raba tallafin kayan abinci ga mazauna jihar domin za su iya daukar matakin ciyar da kawunansu
- Gwamnan da ya bayyana haka a wurin bude kamfanin takin zamani a jihar ya ce duk wanda ya ke son cin abinci ya dauki fatanya ya koma gona ko ya zauna da yunwa
- Amma gwamnatin ta ce a shirye take da taimakawa manoman da kayan bunkasa noma kamar taki, wanda a cewarsa Gombe za ta iya ciyar da Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Gombe - Gwamnatin Gombe ta bayyana cewa ta daina raba tallafin kayan abinci ga mazauna jihar, domin kamata ya yi kowa ya dauki fatanya ya noma abun da zai ci.
Gwamna Inuwa Yahaya ne ya bayyana matakin yayin bude wani kamfanin takin zamanin a jihar, inda ya ce lokaci ya wuce da za a dinga tallafawa mutane da abinci.
Ayi noma ko a rasa abinci a Gombe
Aminiya ta ruwaito cewa Gwamna Inuwa Yahaya ya ce duk wanda ba zai noma abin da zai ci ba, to ya hakura da cin abinci kwata-kwata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce lokaci ya yi da kowa ya kamata ya daina jira sai an ba shi abinci, domin noma ce mafitar da ya kamata kowa ya runguma a jihar.
An rufe kofar raba abinci a Gombe
Gwamna Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya bayyana cewa an kulle kofar bayar da tallafin abinci a jiharsa, domin ba zai lamunci mutane na zaune suna jiran a ba su abinci ba.
Ya ce gwamnatinsa za ta taimakawa duk wanda ya shirya komawa gona domin noma abinci, amma ba zai kara bayar da tallafin abincin ba.
Voice of Nigeria ta wallafa cewa Gwamnan ya ce jiharsa na da fadin kasar da za a iya noma abincin da zai ciyar da Najeriya baki daya.
Za a sarrafa rogo zuwa fetur
A baya mun ba ku labarin cewa gwamnatin Najeriya ta fara kokarin sarrafa rogo zuwa man fetur a wani kokari na bunkasa harkar noma a kasar.
Kwamishinan noma na jihar Enugu, Patrick Ubru ya ce jiharsa da gwamnatin tarayya za su mayar da rogon zuwa sinadarin fetur na 'bioethanol' bayan an noma shi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng