EFCC Za Ta Gurfanar da Ministan Buhari da Ɗan Uwansa a Kotu Kan Tuhume Tuhume 8

EFCC Za Ta Gurfanar da Ministan Buhari da Ɗan Uwansa a Kotu Kan Tuhume Tuhume 8

  • Hukumar EFCC za ta sake gurfanar da ministan sufurin jiragen sama a lokacin mulkin Muhammadu Buhari, Hadi Sirika a gaban kotu
  • Sirika tare da ɗan uwansa za su gurfana a gaban babbar kotun tarayya mai zama a Abuja yau Talata kan wasu tuhume-tuhume shida
  • A makon jiya babbar kotun Abuja ta bada belin Sirika, ɗiyarsa da sauransu kan N100m kowanen su da kuma wasu sharuɗɗa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) za ta gurfanar da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika da dan uwansa yau Talata.

Rahoton Daily Trust ya tattaro cewa EFCC za ta sake gurfanar da tsohon ministan a karo na biyu gaban mai shari'a Balgore na babbar kotun tarayya mai zama a Garki, Abuja.

Kara karanta wannan

Badaƙalar N19.4bn: An samu matsala yayin gurfunar da Ministan Buhari da ɗan uwansa a kotu

Tsohon ministan jiragen sama, Hadi Sirika.
EFCC: Hadi Sirika da ɗan uwansa za su sake gurfana a gaban kotu yau Talata Hoto: Hadi Sirika
Asali: Facebook

Hukumar ta shigar da tuhume-tuhume takwas kan mutanen biyu watau Hadi Sirika da ɗan uwansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan ba ku manta ba Legit Hausa ta kawo maku rahoton cewa wata kotun Abuja ta daban ta amince da belin Sirika da sauran waɗanda ake tuhuma kan kuɗi N100m kowanen su.

Yadda EFCC ta gurfanar da Sirika da ɗiyarsa

Tun da farko, EFCC ta gurfanar da Sirika tare da diyarsa Fatima a gaban mai shari’a Sylvanus Oriji na babbar kotun Abuja, Maitama, ranar Alhamis din da ta gabata.

Sauran waɗanda hukumar ta shigar da ƙara a kansu sune Jalal Hamma da kamfanin Al-Duraq Investment bisa zargin cin amana da satar Naira biliyan 2.7.

A cewar takardar tuhumar, Sirika ya yi amfani da mukaminsa na Ministan Sufurin Jiragen Sama wajen bayar da kwangilar damfara ga diyarsa, surukinsa da abokansa.

Kara karanta wannan

Rusau a Abuja: Gwamnatin Tinubu ta fadi dalilin aniyar rushewa 'yan kasuwa shaguna 500

EFCC ta shigar da tuhume-tuhume shida kan Sirika, diyarsa, surukinsa da sauran waɗanda ake tuhuma a ƙarar farko.

Sirika da ɗiyarsa sun samu beli bisa sharuɗɗa

Yayin da kotun ta bayar da belinsu, ta ce dole ne su kawo mutum biyu da za su tsaya masu waɗanda suka mallaki kadarori a Abuja, The Cable ta ruwaito wannan.

Kotun ta kuma gindaya sharaɗin cewa duk waɗanda za su tsaya masu dole su zama ƴan ƙasa na gari kuma su tabbata sun mallaki takardar shaida daga kotu.

Ta kuma haramtawa dukkan waɗanda ake tuhuma barin ƙasar nan ba tare da izinin kotu ba. Sannan alkalin ya umarci a tsare su a kurkuku har sai sun cika sharuɗɗan.

EFCC za ta gurfanar da Emefiele

A wani rahoton kuma hukumar EFCC ta taso da batun canjin takardun N200, N500 da N1000 wanda Emefiele ya jagoranta a mulkin Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

EFCC ta taso da batun canjin Naira na Buhari, za ta gurfanar da tsohon gwamnan CBN

EFCC za ta gurfanar da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) kan kashe N18.96bn wajen buga sabbin kuɗi N684.5m.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel