EFCC Ta Taso da Batun Canjin Naira Na Buhari, Za Ta Gurfanar da Tsohon Gwamnan CBN

EFCC Ta Taso da Batun Canjin Naira Na Buhari, Za Ta Gurfanar da Tsohon Gwamnan CBN

  • Hukumar EFCC ta taso da batun canjin takardun N200, N500 da N1000 wanda Godwin Emefiele ya jagoranta a mulkin Muhammadu Buhari
  • EFCC za ta gurfanar da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) kan kashe N18.96bn wajen buga sabbin kuɗi na N684.5m
  • Bayan haka kuma hukumar tana zargin Emefiele da karkatar da biliyan sama da 100 daga asusun tara kuɗin shiga na ƙasa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Hukumar yaki da masu yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) za ta sake gurfanar da tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Godwin Emefiele a ranar Laraba.

A wannan karon EFCC za ta gurfanar da Emefiele ne kan biyan N18.96bn a matsayin kuɗin buga N684m na sababbin takardun Naira da ya canja, Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

EFCC za ta gurfanar da Ministan Buhari da ɗan uwansa a kotu kan tuhume-tuhume 8

Tsohon gwamnan CBN, Emefiele a kotu.
EFCC za ta maka tsohon gwamnan CBN a gaban kotu kan canjin Naira Hoto: Mr Godwin Emefiele
Asali: Twitter

Tun da farko dai an shirya gurfanar da shi a ranar 30 ga Afrilu, 2024, amma aka sake dage zaman bayan yarjejeniyar da kotu da bangarorin suka cimma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da wasu laifuffuka ake zargin Emefiele?

A tuhume-tuhume huɗu da ta shigar gaban kotu, hukumar EFCC ta zargi tsohon gwamnan babban bankin da shure umarnin doka wajen aiwatar da tsarin canjin kuɗi.

EFCC ta tuhumi Emefiele da cewa ya sa ƙafa ya shure tanadin doka domin jefa al'umma cikin baƙar wahala yayin ƙaƙaba masu tsarin canjin kuɗi a gwamnatin Muhammadu Buhari.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kuma zargi Emefiele da wawure Naira biliyan 124.8 daga asusun tara kudaden shiga na tarayya.

Za a gurfanar da tsohon gwamnan na CBN kan wadannan tuhume-tuhume a gaban mai shari’a Maryam Anenih ta babbar kotun birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya shiga muhimmin taro a Villa, ya rantsar da sababbin kwamishinoni 2

Kararrakin da aka shigar kan Emefiele

Wannan shari’ar dai za ta sa adadin kararrakin da aka shigar da Emefiele a gaban kotu su zama uku, rahoton Leadership.

A ranar 17 ga Nuwamba, 2023, Emefiele ya gurfana a gaban mai shari’a Hamza Muazu a kan tuhume-tuhume shida da suka hada da damfara wanda ya ki amsa laifin.

An kuma zarge shi da cin amana a ofishinsa ta hanyar amincewa da kwangilar sayen motoci 43 da suka kai Naira biliyan 1.2 daga shekarar 2018 zuwa 2020.

Kotu ta kori bukatar Yahaya Bello

A wani rahoton na daban Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya yi rashin nasara a yunkurin dakatar da shari'ar da ake masa kan badakalar N80bn.

Babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta yi watsi da bukatar tsohon gwamnan saboda bai halarci zaman shari'a ba ranar Jumu'a.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel