Bola Tinubu Ya Shiga Muhimmin Taro a Villa, Ya Rantsar da Sababbin Kwamishinoni 2
- Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci taron majalisar zartarwa (FEC) karo na biyar a 2024 a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja ranar Litinin
- Gabanin fara taron, majalisar ta yi shiru na tsawon minti ɗaya domin girmama tsofaffin ministoci biyu da suka kwanta dama
- Haka nan Bola Tinubu ya rantsar da ƙarin kwamishinoni biyu na hukumar ƙidaya ta ƙasa (NPC) kafin a fara taron a Villa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu na jagorantar taron majalisar zartarwa ta ƙasa (FEC) yanzu haka a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
Taron wanda shi ne karo na biyar tun daga watan Janairun 2024, ana sa ran zai fito da wasu shawarwarin da za a tunkari wasu kalubalen da suka addabi kasar.
Tinubu ya rantsar da kwamishinonin NPC 2
Kafin a fara taron Mai girma Bola Tinubu ya rantsar da ƙarin kwamishinonin hukumar kidaya ta kasa (NPC) guda biyu, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Waɗanda Shugaban kasa Tinubu ya rantsar sun haɗa da Mista Fasuwa Johnson daga jihar Ogun da kuma Dokta Amid Tadese Raheem daga jihar Osun.
A ranar 8 ga Nuwamba, 2023, Tinubu ya nada kwamishinonin guda 20 a hukumar kidaya NPC, inda tara daga cikinsu sun sake komawa ne zango biyu.
Kafin yau, kwamishinoni 17 daga ciki sun karɓi rantsuwar kama aiki ranar 14 ga watan Maris, cewar rahoton The Nation.
FEC: Karrama tsofaffin ministocin da suka rasu
Gabanin fara taron FEC yau Litinin, majalisar zartarwar ta yi shiru na tsawon minti ɗaya domin karrama tsofaffin mambobi biyu da suka rasu, Farfesa Fabian Osuji da Cif Ogbonnaya Onu.
Osuji, mai shekaru 82, wanda ya rasu a ranar 28 ga Fabrairu, 2024, ya rike mukamin ministan ilimi daga Yuli 2003 zuwa Maris 2005 a gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.
A ɗaya bangaren, Onu, gwamnan farar hula na farko a jihar Abia, ya rike mukamin ministan kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire a gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Onu ya rasu ne ranar 11 ga watan Afrilu, 2024 yana da shekaru 72 a duniya.
Waɗanda suka halarci taron FEC
Daga cikin wadanda suka halarci taron FEC akwai mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da sakataren gwamnatin tarayya, George Akume.
Shugaban ma'aikatar fadar gwamnatin Najeriya, Femi Gbajabiamila, da shugabar ma'aikatan gwamnatin tarayya, Dakta Folasade Yemi-Esan da ministoci da dama sun halarci taron.
Mamban PDP-BoT ya koma APC
A wani rahoton na daban Charles Idahosa, tsohon ɗan kwamitin amintattun PDP ya koma jam'iyyar All Progressive Congress (APC) a jihar Edo.
Tun ranar 29 ga watan Afrilu, 2024, jigon ya bayyana ficewarsa daga jam'iyyar PDP tare da nadamar abin da ya aikata a baya.
Muhammad Malumfashi, babban editan sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng