"Wannan ai Sata ce," NLC ta Magantu kan Karin Kudin Wutar Lantarki a Kogi

"Wannan ai Sata ce," NLC ta Magantu kan Karin Kudin Wutar Lantarki a Kogi

  • Kungiyar kwadago ta NLC a jihar Kogi ta kamanta karin kudin wuta da sata da tsakar rana daga hannun 'yan Najeriya da ke cikin mawuyacin hali kafin yanzu
  • Shugaban kungiyar reshen jihar, Kwamred Gabriel Amari ne ya fadi haka a ofishin rarraba hasken wutar lantarkin Abuja dake aiki a Lokoja yayin da ake zanga-zanga yau
  • Ya ce alamu na nuna cewa gwamnatin tarayya ba ta damu da halin matsin da ‘yan Najeriya ke ciki ba ko kadan domin a gwamnatin nan ne aka raba ajin masu amfani da wutar

A'isha Ahmad editak ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Kogi- Shugaban kungiyar kwadago reshen jihar Kogi, Kwamred Gabriel Amari, ya bayyana karin kudin wutar lantarki da sata da tsakar rana.

Kara karanta wannan

Wahalar Rayuwa: Ka da a Karaya da Mulkin Bola Tinubu, Jigon APC Ya Lallabi Mutane

Ya bayyana hakan ne yayin da kungiyar ta rufe ofishin rarraba hasken wutar lantarkin Abuja dake aiki a Lokoja yau Litinin, kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Kungiyar NLC
NLC a Kogi ta bayyana karin kudin wuta da sata Hoto:@NLCHeadquarters
Asali: Twitter

Shugaban ya ce dole ne gwamnati ta yi gaggawar dawo da kudin wutar yadda ya ke a baya domin saukakawa talakawan Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Gwamnati ba ta damu ba,” NLC

Shugaban NLC reshen jihar Kogi, kwamred Gabriel Amari ya ce matakan da gwamnatin tarayya ke dauka na nuna ba ta damu da halin da takawanta ke ciki ba.

Ya bayyana cewa a karkashin gwamnatin Bola Tinubu ne kawai aka samu karin kudin wuta dai-dai da karfin wadanda za su sha wutar.

Kwamred Amari ya jaddada cewa ‘yan kasar nan na shan wahala sosai da sababbin tsare-tsaren da gwamnati ke bijiro da su.

Ya kara da cewa lokaci ya yi da gwamnati za ta saurari korafe-korafen ‘yan Najeriya da zimmar magance su.

Kara karanta wannan

Kayayyaki za su kara tsada a Najeriya, an kara harajin shigo da kayan kasar waje

Kungiyar ta NLC tun da fari ta bayyana cewa karin kudin wuta a kasar nan bai dace ba, kamar yadda The Nation ta wallafa.

Kudin wuta: Kungiyar Kwadago ta fusata

A baya mun labarta muku cewa kungiyar kwadago a Najeriya ta fusata kan yadda gwamnatin tarayya ta kara farashin hasken wutar da ‘yan kasa ke sha.

A ranar Litinin ne kungiyar NLC ta jagoranci zanga-zangar da ta kai ga rufe wasu kamfanonin rarraba hasken wutar a jihohin kasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban editan sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel