‘Yan Kasuwa Sun Fara Saida Fetur a Sabon Farashi Yayin da Lita Ta Koma N770 a Depo

‘Yan Kasuwa Sun Fara Saida Fetur a Sabon Farashi Yayin da Lita Ta Koma N770 a Depo

  • Kungiyar dillalan man fetur (IPMAN) ta bayyana cewa tsadar man fetur ta biyo bayan karin kudin da aka samu a depo-depo na man
  • ‘Yan kasuwar sun ce masu depo depo sun kara farashin man fetur zuwa Naira 770 kan kowace lita, lamarin da ya jawo su ma suka yi karin
  • A cewar masu sayar da man, farashin dakon man a fadin kasar nan ma ya yi tashin gwauron zabo, wanda shi ma ya kara jawo tsadar man

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kungiyar dillalan man fetur ta kasa (IPMAN) ta bayyana cewa masu tashoshin mai (masu zaman kansu) sun kara kudin fetur zuwa Naira 770 kan kowace lita.

Kara karanta wannan

Adamawa: Kwastam ta kama jiragen ruwa makare da man fetur za a kai kasashen waje

Shugaban IPMAN na kasa, Abubakar Maigandi ne ya bayyana hakan, inda ya bayyana cewa masu depo-depo na korafin cewa farashin dakon fetur ya karu.

An kara kudin man fetur zuwa N800 da N1000 kan kowace lita
‘Yan kasuwa sun ba da rahoton hauhawar farashin man fetur a depo-depo, ya koma N770/lita. Hoto: Bloomberg/Contributor
Asali: Getty Images

"Kudin dakon fetur ya karu" - IPMAN

Maigandi ya ce karuwar kudin dakon fetur ya yi tasiri ga farashin man fetur a fadin kasar duk da yanzu yana samuwa sosai, jaridar The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban na kungiyar IPMAN ya ce karin kudin dakon ya haifar da sauye-sauyen farashin man fetur, wanda ya shafi farashin da gidajen mai ke bayarwa.

A cewarsa, farashin dakon fetur a Legas ya kai kusan N30 ko N35 kan kowacce lita, yana mai jaddada cewa kudin man fetur a Legas ya kai N800 kan kowace lita yanzu.

'Yan kasuwa sun kara kudin fetur

Maigandi ya ce masu dakon man fetur daga jihar Kebbi na biyan kudin da ya kai N70 a kowace lita, wanda hakan ya sa ake sayar da mai a kan N900 da kuma N1,000 kan kowace lita a Kebbi.

Kara karanta wannan

Matakai 5 da Gwamnatin Tinubu ta dauka da suka jefa ‘yan Najeriya a wahalar rayuwa

A cewar Maigandi:

“Yanzu akwai man saboda an rage yawan masu siya. Amma matsalar ita ce masu depo sun kara kudi. Yanzu suna ba da lita 1 a kan N770.
“A wannan yanayin, farashin fetur din zai danganta da garin da mutum yake. A jiha mafi kusa kamar Lagos, za ka biya kudin dako N30, ka ga lita za ta koma N800 kenan.

Ya ce farashin man fetur ba zai taba yin kasa ba har sai Dangote da sauran matatun mai a fadin Najeriya sun fara samar da shi har ya wadata.

Al-Mustapha ya gargadi Tinubu kan fetur

A wani labarin, mun ruwaito maku cewa dogarin tsohon shugaban kasa, Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha (mai ritaya) ya gargadi gwamnatin Bola Ahmed Tinubu kan yin wasa da harkar fetur.

A cewar Hamza Al-Mustapha, duk shugaban kasar da ya taba fetur to ba ya yin karo a mulkin kasar, don haka ya nemi Tinubu da ya yi hattara da ‘yan kasuwa.

Muhammad Malumfashi, babban editan sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel