'An Ba Ni Kudi in Sa Hannu a Tsige Gwamnan Jiharmu', Tsohon Kakakin Majalisa

'An Ba Ni Kudi in Sa Hannu a Tsige Gwamnan Jiharmu', Tsohon Kakakin Majalisa

  • Tsohon kakakin majalisar jihar Ribas, Edison Ehie, ya fallasa irin kullalliyar da aka kulla domin tsige Gwamna Siminalayi Fubara
  • Mr Ehie ya tariyo yadda aka rika ba 'yan majalisar jihar makudan kudade domin su sa hannu a tsige gwamnan jihar na Rivers
  • A yayin da ya ki karbar kudin, Mr Ehie ya ce an kulla masa makirci wanda ya ja har 'yan sanda suka fara nemansa ruwa a jallo

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Rivers - Tsohon kakakin wani tsagi na majalisar dokokin jihar Rivers, Edison Ehie, ya bayyana cewa an yi masa tayin kudi domin tsige Gwamna Siminalayi Fubara.

An ba 'yan majalisa kudi domin su tsige gwamnan jihar Rivers
Tsohon kakakin majalisar Rivers, ya tariyo yadda aka basu kudi domin su tsige Gwamna Fubara. Hoto: AmaopuSim, Ehie Edison
Asali: Facebook

"An ba da kudi a tsige Fubara" - Ehie

Kara karanta wannan

George-Kelly Alabo: Dalilin da ya sa na yi murabus daga kwamishinan ayyuka na jihar Rivers

Ehie Edison wanda shi ne shugaban ma’aikatan Gwamna Fubara a yanzu, ya kasance shugaban masu rinjaye a majalisar lokacin da aka fara yunkurin tsige Fubara, jaridar The Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake magana a wani taron da aka gudanar a yankin Ahoada ta Gabas na jihar Rivers a karshen mako, Ehie, ya ce an yi masa tayin kudi domin ya tsige gwamnan.

Shi da wasu ‘yan tsiraru a majalisar sun nuna rashin amincewarsu da matakin, lamarin da ya tilasta musu ballewa daga cikin ‘yan majalisar da ke goyon bayan Nyesom Wike.

Zaman sulhu ya rushe a Rivers

Daga baya ne Ehie ya zama kakakin wani tsagi bayan majalisar ta dare gida biyu, amma aka rushe shugabancinsa bayan shugaban kasa Bola Tinubu ya shiga tsakani.

Sai dai yunkurin samar da zaman lafiya ya ruguje bayan wani dan kankanin lokaci kuma bangarorin biyu suka koma ba sa ga maciji.

Kara karanta wannan

Gwamna Fubara ya ɗauki zafi, ya canza wurin zaman majalisar dokokin jihar Rivers

'Yan sanda sun nemi Ehie ruwa a jallo

Ko da yake Mr Ehie bai bayyana sunayen wadanda suka ba shi kudin ba, amma ya ce ya ki karbar tayin, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto.

“Sun ba ni dukkanin kuɗin da aka ɓoye a baya, wanda na ƙi karba. Ganin haka ya sa suka hada kai da jami'an tsaro aka fara nema na ruwa a jallo."

- Ehie Edison

A shekarar 2023, ‘yan sanda sun bayyana cewa suna neman Edison Ehie ruwa a jallo, kan zargin yana da hannu a mamayar da aka kai majalisar dokokin jihar.

An yi zanga-zanga a Port Harcourt

A wani labarin, mun ruwaito maku cewa wasu jiga-jigan jam'iyyar APC a jihar Rivers, sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da gwamnan jihar, Siminalayi Fubara.

Masu zanga-zangar sun mamaye ginin gidajen 'yan majalisu da ke a majalisar jihar, inda suka yi zargin Fubara na shirin rushe gidajen ba tare da wani kwakkwaran dalili ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel