Karin Kudin Wuta: Kungiyar Kwadago za ta Rufe Ofisoshin Rarraba Hasken Lantarki

Karin Kudin Wuta: Kungiyar Kwadago za ta Rufe Ofisoshin Rarraba Hasken Lantarki

  • Kungiyar kwadago ta yi barazanar rufe ofisoshin kamfanonin raba lantarki a fadin kasar nan, har sai gwamnatin tarayya ta janye karin kudin wutar da ta yi a baya-bayan nan
  • A baya, gwamnati ta bayar da sanarwar karin farashin lantarki daga N65 zuwa N225 kan kowanne kilowatt ga masu amfani da wutar a rukunin farko
  • Daga bisani ta rage wani kashi daga abun da aka kara, wanda shi ma kungiyoyin kwadago su ka yi watsi da shi, tare da bukatar soke karin bakidaya kafin 12 ga watan Mayu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja-Kungiyar kwadago ta NLC ta yi barazanar rufe ofisoshin kamfanonin raba lantarki a fadin kasar nan, har sai gwamnatin tarayya ta janye karin kudin wutar da ta yi a baya-bayan nan.

Kara karanta wannan

"Wannan ai sata ce," NLC ta magantu kan karin kudin wutar lantari a Kogi

Idan za a iya tunawa dai gwamnati ta bayar da sanarwar karin farashin lantarki daga N65 zuwa N225 kan kowanne kilowatt ga masu amfani da wutar a rukunin farko.

Kungiyar NLC
Kungiyar kwadago ta yi barazanar rufe ofisoshin kamfanonin rarraba hasken wuta Hoto: @NLCHeadquarters
Asali: Twitter

Daga bisani ta rage wani kashi daga abn da aka kara, wanda shi ma kungiyoyin kwadago su ka yi watsi da shi, tare da bukatar soke karin bakidaya kafin 12 ga watan Mayu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani abu da kungiyoyin suka bukata shi ne watsi da tsarin mayar da masu hulda da kamfanonin lantarkin aji-aji, kamar yadda Channels Television ta wallafa.

NLC ta nemi soke karin kudin wuta

Kungiyar kwadago ta NLC ta yi barazanar rufe wasu ofisoshin kamfanonin rarraba hasken wutar lantarki a jihohin Najeriya domin nuna rashin goyon baya ga karin farashin kudin wuta.

Ma’ajin kungiyar NLC na kasa, Olatunji Ambali da mataimakin shugaban kungiyar ‘yan kasuwa ta TUC, Tommy Etim sun bayyana cewa dole ne a dawo da farashin wutar lantarki yadda yake a baya.

Kara karanta wannan

Wutar lantarki: 'Yan kwadago sun fusata, sun rufe ofishin hukumar NERC a Abuja

Ana sa ran ‘ya’yan kungiyar kwadagon za su rufe hukumar dake kula da hasken wutar lantarki ta NERC, da ma’aikatar hasken lantarki, da ofisoshin kamfanonin rarraba hasken wutar a wasu jihohin Najeriya.

An fara rufe kamfanin wuta a Jos

Mun kawo muku labarin cewa kungiyar kwadago ta NLC ta jagoranci zanga-zangar rashin amincewa da karin kudin wutar lantarki a wasu sassan Najeriya.

Zuwa yanzu, kungiyar ta garkame kamfanin rarraba hasken wuta na DisCo dake Jos a jihar Plateau, inda yan kungiyar suka shiga rufe bakin kamfanin domin nuna kin jinin karin kudin.

Muhammad Malumfashi, babban editan sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel