NNPC Ya Fara Hako Mai a Sabuwar Rijiya a Kudancin Najeriya
- Kamfanin man fetur na kasa (NNPC) tare da haɗakar kamfanin Olifield Services sun fara hako mai a sabuwar rijiya
- NNPC ya kuma bayyana cewa sabuwar rijiyar mai suna OML 13 za ta rika fitar da ganguna 40,000 a kowace ranar duniya
- A rahoton da kamfanin ya fitar ya nuna cewa tuni shi da abokan hulɗarsa suka fara samar da mai ganguna 6,000 a rijiyar
Kamfanin hakar man fetur na Najeriya (NNPC E & P) da ke matsayin reshen kamfanin NNPC tare da haɗakar kamfanin mai na NOSL sun sanar da fara hako man fetur a sabuwar rijiya.
A wace jiha aka fara hako man?
Rahotanni sun nuna cewa sabuwar rijiyar da aka fara hako man tana jihar Akwa Ibom ne da ke kudancin Najeriya.
Kamfanin ya bayyana sanarwar ne a jiya Lahadi, 12 ga watan Mayu cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yaushe aka fara hako man?
Takardar mai dauke da sa hannun jami'in yada labaran kamfanin Olufemi Soneye ta nuna cewa an fara hako mai dinne tun ranar 6 ga watan Mayu.
An fara hako mai ganga 6,000 a farkon lamarin kafun daga bisani kamfanin ya kara kaimi wurin aikin.
Ana sa ran cewa daga nan zuwa ranar 27 ga watan Mayu kamfanin zai fara hako gangunan mai 40,000.
Amfanin sabuwar rijiyar man
A cewar jami'in, wannan haɗaka da ke tsakanin kamfanonin ita ce ta farko wanda kuma ta kawo cigaba sosai ga tattalin Najeriya.
Kamfanin ya kuma bayyana cewa hadakar za ta cimma samar da wadataccen mai domin amfanin yau da kullum a fadin ƙasar nan.
Makomar al'ummar yankin da rijiyar ta ke
Dangane da abin da ya shafi al'ummar yankin kuma, kamfanin ya ce ba za a barsu a baya ba wurin cin arzikin.
A lokutan hakar man ya nuna cewa za a tabbatar da tsaftace yankin tare da tabbatar da cewa mutanen sun ci moriyar aikin.
Majalisa ta dauki mataki kan wahalar mai
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Opeyemi Bamidele, ya bayar da tabbacin kawo karshen matsalar karancin man fetur a Najeriya nan gaba kadan.
Ya ce bangaren majalisa yana aiki babu gajiyawa wajen ganin an magance dogayen layuka a gidajen mai da tsadarsa a kasar nan cikin gaggawa.
Asali: Legit.ng