Zargin Rusa Gidajen ’Yan Majalisa: Magoya Bayan Wike Sun Fita Zanga Zanga a Port Harcourt

Zargin Rusa Gidajen ’Yan Majalisa: Magoya Bayan Wike Sun Fita Zanga Zanga a Port Harcourt

  • A yayin da 'yan majalisar Rivers ke kara kausasa zargi kan gwamnan jihar na zai rusa gidajen majalisa, zanga-zanga ta barke a Port Harcourt
  • Wasu jiga-jigan jam’iyyar APC na jihar da ke goyon bayan Nyesom Wike ne suka gudanar da zanga-zangar ta nuna adawa da Fubara
  • Da yake jawabi, shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai, Kingsley Chinda ya ce sun gano gine-ginen za su yi aiki har nan shekara 25

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Rivers - A yammacin yau Lahadi ne wasu fitattun jiga-jigan jam’iyyar APC na jihar Rivers suka gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga majalisar jihar da ke Port Harcourt.

An yi zanga-zangar nuna adawa da Gwamna Fubara a Port Harcourt
Rivers: MAgoya bayan Wike sun gudanar da zanga-zangar adawa da Fubara a Port Harcourt. Hoto: Ja'afar Galadima
Asali: Facebook

Mutanen Wike sun yi zanga-zanga

Kara karanta wannan

Mazauna Port Harcourt sun damu da rikicin Wike da Fubara, sun mika bukata ga alkalai

Fitattun ‘yan jam’iyyar APC irin su Desmond Akawor, Kingsley Chindah, Olaka Nwogu, Cif Tony Okocha, da dai sauransu na cikin zanga-zangar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Daily Trust ta ruwaito masu zanga-zangar na nuna adawa da wani shiri da su ke zargin Gwamna Fubara na yi na rusa gidajen 'yan majalisu da ke cikin majalisar.

Masu zanga-zangar sun samu tarbar Hon. Martins Amaehwule, kakakin majalisar mai biyayya ga Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya (FCT).

Wike na shirin rusa gidajen majalisa?

Amaewhule ya shaida wa masu zanga-zangar cewa akwai wani gagarumin shiri da gwamna Siminalayi Fubara ya yi na ruguza gine-gine a cikin majalisar.

Ya ce Fubara na son ya rusa gine-gine ba tare da wani abu da ya samu gidajen majalisar ba kuma a halin yanzu ‘yan majalisar da iyalansu ne ke amfani da su.

Kara karanta wannan

Jami’an Birtaniya sun yi watsi da Yarima Harry a ziyarar da ya kawo zuwa Najeriya

Amaewhule ya ce ‘yan majalisar ba su taba gayyatar gwamnan ya zo bangaren gidajen zaman su ba, inda ya kara da cewa gidajen mallakin majalisar dokokin jihar ne ba na gwamna ba.

Kakakin majalisar a yayin da ya ke nunawa masu zanga-zangar gine-ginen gidajen majalisar, ya dage kan cewa gwamnan ba shi da hurumin bayar da umarni ga ‘yan majalisar na inda za su yi zamansu.

"Dalilin gudanar da zanga-zangar" - Chinda

Shugaban marasa rinjaye na majalisar wakilai, Kingsley Chinda, a lokacin da yake bayyana makasudin ziyarar tasu, ya ce sun damu matuka da rahotannin sake ruguza ginin majalisar.

Chinda ya ce kafin ziyarar tasu, sun riga sun tuntubi kwararru domin tantance ingancin gine-ginen, kuma rahoton nasu ya nuna cewa za su dau fiye da shekaru 25 ana amfani da su.

Ya ce gine-ginen da da Wike ya yi na majalisar kimanin shekaru biyu da suka gabata sun kasance mafi kyau a Afirka kuma sun fi tsari a kan gine-ginen majalisar dokoki ta kasa.

Kara karanta wannan

Gwamna Fubara ya ɗauki zafi, ya canza wurin zaman majalisar dokokin jihar Rivers

Sakon mazauna Port Harcourt ga alkalai

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel