'Yan Bindiga Sun Kashe ’Yan Sanda 4 da Jami’an FRSC a Wani Kazamin Hari a Enugu

'Yan Bindiga Sun Kashe ’Yan Sanda 4 da Jami’an FRSC a Wani Kazamin Hari a Enugu

  • ‘Yan ta’adda sun kashe jami’an tsaro a jihar Enugu yayin da suka kai kazamin hari a cikin kwanaki biyu
  • An hallaka ‘yan sanda da jami’an FRSC a jihar ta Enugu, gwamna ya sha alwashin daukar mataki nan ba da jimawa ba
  • A jihohin Kudancin Najeriya ne ake yiwa jami’an tsaro kisan gilla ba tare da wani daukar matakin da ya dace ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Jihar Enugu - An samu aukuwar aikin ta'addanci a yankunan Orba da Eha-Alumona a kananan hukumomin Udenu da Nsukka na jihar Enugu.

Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, wasu ‘yan bindiga ne suka kai hari kan jami’an ‘yan sandan Najeriya da FRSC ranar Asabar da ta gabata.

Kara karanta wannan

Ta'asar 'yan bindiga ta kai mutuwar mutane 4 da basu ji ba basu gani ba a Benue

An kai harin ne sa’o’i 24 bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai wa ‘yan sanda hari tare da kashe su a ranar Juma’a a babban birnin jihar.

'Yan ta'adda sun kashe jami'an tsaro
'Yan ta'adda sun kashe jami'an tsaro a jihar Enugu | Hoto: Muhammad Isa
Asali: Getty Images

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka kai harin da yamma

Wakilin Punch ya tattaro cewa, an sake kai hari na biyun ne a a ranar asabar a magamar Premier da ke Eha-Alumona a karamar hukumar Nsukka da misalin karfe 4 na yamma.

An hallaka jami’an hudu ne a harin, inda wasu kuma suka samu munanan raunuka a sakamakon aikin ta’addancin.

Tsagerun ‘yan bindigan sun kuma farmaka tare da kone mota kirar Hilux mallakin basaraken gargajiya na Egali Amalla a karamar hukumar Udenu, Patrick Eze wanda aka fi sani da Igwe Waziri.

Rahotanni sun bayyana cewa, basaraken da harin ya rutsa dashi ya samu nasarar tsere cikin ikon Allah babu rauni, Sahara Reporters ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Mazauna Port Harcourt sun damu da rikicin Wike da Fubara, sun mika bukata ga alkalai

‘Yan bindigar sun kuma kona wata mota jami’an FRSC, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Martanin ‘yan sanda game da lamarin

A halin da ake ciki an tuntubi kwamishinan ‘yan sandan jihar, Kanayo Uzuegbu, game da lamarin ya ce bai san da labarin ba, inda yace a tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan jihar.

Sai dai kokarin samun bayani daga kakakin rundunar, Daniel Ndukwe ya ci tura, domin bai amsa kiran da aka yi masa ba, kuma bai mayar da sakon sakon tes da aka tura masa ba.

Gwamna Peter Mbah na jihar Enugu ya sha alwashin cafke maharan da suka kashe jami’an tsaron Najeriya da suka kashe.

'Yan bindiga sun hallaka jama'a a Benue

A wani labarin, wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane hudu a yankin Mbachon da Mbagbe a yankin Turan, unguwar Yaav da ke karamar hukumar Kwande a jihar Benue a ranar Juma’a, 10 ga watan Mayu.

Kwande dai wanki ne a shiyyar Sanatan Benue ta Arewa maso Gabas kuma al’ummomin biyu da abin ya shafa suna kan iyaka da jihar Taraba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel