George-Kelly Alabo: Dalilin da Ya Sa Na Yi Murabus Daga Kwamishinan Ayyuka Na Jihar Rivers

George-Kelly Alabo: Dalilin da Ya Sa Na Yi Murabus Daga Kwamishinan Ayyuka Na Jihar Rivers

  • Tsohon kwamishinan ayyuka a Rivers, Alabo George-Kelly, ya bayyana dalilin ajiye mukaminsa na kwamishina
  • Alabo, wanda yaron siyasar Nyesom Wike ne, ya zargi da Gwamna Siminalayi Fubara da kashe kudi ba tare da kasafi ba
  • Tsohon kwamishinan ya bayyana cewa ya ji tsoron kada a kama shi da laifin bayar da kwangiloli ba bisa ka'ida ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Rivers - Tsohon kwamishinan ayyuka a Rivers, Alabo George-Kelly, ya ce ya yi murabus daga mukarraban Siminalayi Fubara, gwamnan Rivers, saboda jihar na kashe kudade ba tare da wani lissafi ba.

George-Kelly Alabo ya fadi dalilin yin murabus daga mukarraban Fubara
Rivers: Tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Rivers, Alabo ya fadi dalilin da ya sa ya yi murabus. Hoto: George-Kelly Alabo
Asali: Facebook

sTsohon kwamishinan ayyuka a Rivers, Alabo George-Kelly‘Yan majalisa biyar masu biyayya ga Fubara sun amince da Naira biliyan 800 a matsayin kasafin kudin jihar na shekarar 2024.

Kara karanta wannan

Matakai 5 da Gwamnatin Tinubu ta dauka da suka jefa ‘yan Najeriya a wahalar rayuwa

Mun ruwaito cewa wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta soke kasafin tare da kuma hana Fubara yin katsalandan a lamuran majalisar jihar Rivers.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ki amincewa da kasafin kudin Rivers

Kotun ta bukaci gwamnan da ya sake gabatar da kasafin kudin ga majalisar da aka kafa karkashin kakakin majalisar, Martin Amaewhule, in ji rahoton The Cable.

Amaewhule na biyayya ne ga Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya (FCT).

A wani bangare na yarjejeniyar zaman lafiya da Shugaba Bola Tinubu ya kulla a yunkurin sasanta Wike da Fubara, an amince da cewa za a sake gabatar da kasafin kudin.

A wata hira da ya yi da gidan Talabijin na Channels, Alabo ya ce Gwamna Fubara ya karya doka a lokacin da ya rika bayar da kwangiloli a yayin da babu kasafin kudi.

Kara karanta wannan

Rayuwa za ta yi sauki kuma abinci zai wadata a mulkina, Tinubu ya dauki alkawari

"Dalilin da sa na yi murabus" - Mr Alabo

Mr Alabo ya bayyana ce:

“Wani bangare na yarjejeniyar shi ne a sake gabatar da kasafin kudin ga majalissar jihar. Har yau ba a yi hakan ba. To don me za a rika ba da kwangila alhalin babu kasafi?
“Ta yaya zan yi aiki karkashin irin wannan gwamnati wadda za ta sa in rika sa hannu kan takardun bayar da kwangiloli alhalin na san ina karya doka? Ba zan iya ba.
“Ni na san matsayi na na kwamishina ba ni da wata kariya daga tuhuma, kenan wata rana za a iya kama ni. Wata kila wannan ne dalilin da ya sa na yi murabus."

George-Kelly ya kara da cewa yau, gobe, jibi, ko ma yaushe ne zai ci gaba da yin biyayya ne kawai ga uban gidansa a siyasa, Nyesom Ezenwo Wike.

Rikicin Rivers: Mazauna Port Harcourt sun damu

Kara karanta wannan

An zargi wani jami'in KEDCO da kashe abokinsa saboda abin duniya

A wani labarin, mun ruwaito maku cewa mazauna Port Harcourt, babban birnin jihar Rivers sun nuna damuwa kan yadda rikicin jihar ya ki ci ya ki cinyewa.

Wani lauya, Aghogho Okpako ya yi kira da a gaggauta yanke hukunci kan shari’o’in da ke da alaka da rikicin siyasa a jihar domin kawo karshen matsalolin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.