Ta’asar ’Yan Bindiga Ta Kai Mutuwar Mutane 4 da Basu Ji Ba Basu Gani Ba a Benue
- ‘Yan ta’adda sun tafka barna a wani yankin jihar Benue, lamarin da ya kai ga mutuwar mutane hudu nan take
- Rahoto ya bayyana cewa, an sace wani mutum bayan da tsagerun suka farmaki jama’a da yammacin 10 ga watan Mayu
- Jihar Benue na daga cikin jihohin Arewacin Najeriya da ke yawan fuskantar hare-hare da tashe-tashen hankula
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas
Jihar Benue - Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutane hudu a yankin Mbachon da Mbagbe a yankin Turan, unguwar Yaav da ke karamar hukumar Kwande a jihar Benue a ranar Juma’a, 10 ga watan Mayu.
Kwande dai wanki ne a shiyyar Sanatan Benue ta Arewa maso Gabas kuma al’ummomin biyu da abin ya shafa suna kan iyaka da jihar Taraba.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 5 na yamma lokacin da mutane ke shirin komawa zuwa matsugunan su daban-daban bayan hada-hadar ranan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shaida daga bakin mazaunin yankin a Benue
Wani mazaunin unguwar, Lawrence Akeregba y ace:
“Sun afkawa al’ummomin biyu ne da misalin karfe 5 na yamma, suka budewa mutane wuta, a lokacin da kura ta lafa aka samu sun harbe mutane hudu har lahira.”
Lawrence Akerigba ya shaidawa jaridar The Nation cewa an dauki gawa daya domin binne shi, yayin da uku suka bace, an kuma tafi da wani mutum daya.
Karamar hukumar Kwande dai tana da iyaka da jihar Taraba kuma ta shafe shekaru 15 tana fuskantar hare-haren ta’addanci.
Yadda makiyaya suka kwace wani yankin Benue
Ya kara da cewa:
“A gundumar Moon da ke karamar hukumar Kwande, jama’a sun shafe shekaru 16 ba su samu damar zuwa gonakinsu ba saboda gaba daya makiyaya sun mamaye yankin, inda suka mayar da shi wurin kiwo ga dabbobinsu.”
Da aka tuntubi rundunar ‘yan sandan jihar, ta ce har yanzu ba ta samu rahoton kashe-kashen ba.
'Yan bindiga sun kashe mutum 20 a Zamfara
A wani labarin, miyagun 'yan bindigan daji sun halaka "akalla mutum 20" da suka kunshi magidanta maza da mata da kananan yara a kauyen Bilbis da ke jihar Zamfara.
Yayin wannan mummunan harin, 'yan ta'addan sun jikkata wasu mutum bakwai wadanda yanzu haka suke kwance suna jinya a asibiti.
Asali: Legit.ng