An Shiga Fargaba Bayan Jirgin Sama Daga Abuja Zuwa Lagos Ya Ci Karo da Cikas, Ya Fantsama Daji

An Shiga Fargaba Bayan Jirgin Sama Daga Abuja Zuwa Lagos Ya Ci Karo da Cikas, Ya Fantsama Daji

  • An shiga fargan bayan wani jirgin sama ya sake samun matsala a filin tashi da saukar jiragen sama da ke jihar Lagos
  • Lamarin ya faru ne a yau Asabar 11 ga watan Mayu yayin da jirgin ya fantsama cikin daji a kokarin tsayawa
  • Jirgin mai dauke da fasinjoji 52 ya taso ne daga birnin Abuja zuwa Lagos lokacin da ya hadu da wannan tsautsayi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - Wani jirgin sama dauke da fasinjoji 52 ya gamu da tsautsayi bayan ya kauce hanya a jihar Lagos.

Jirgin, mallakin Xejet Airlines ya kauce hanya ne tare da fantsama cikin daji a cikin filin jirgin saman Lagos.

Kara karanta wannan

Matakai 5 da Gwamnatin Tinubu ta dauka da suka jefa ‘yan Najeriya a wahalar rayuwa

Jirgin sama ya sake cin karo da cikas a Lagos
Mutane sun shiga tsoro bayan jirgin sama ya kauce hanya Lagos. Hoto: FRCN.
Asali: UGC

Daga ina jirgin ya dauko fasinja?

The Nation ta tattaro cewa jirgin ya dauko fasinjoji ne daga birnin Tarayya Abuja zuwa jihar Lagos.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'an Hukumar kula da jiragen saman ta FAAN sun yi gaggawar kai dauki wurin domin ceto fasinjoji, cewar Daily Trust.

Kamfanin jiragen Xejet na kasuwanci ne da ke filin tashi da saukar jiragen saman Murtala Mohammed a Lagos.

Wata majiya ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce tsautsayin ya faru ne da misalin karfe 11:29 na rana.

Jami'ai sun kawo dauki ga fasinjoji

"Wani jirgin sama mallakin Xejet Airlines ya sake kauce hanya a filin tashi da saukar jiragen saman Lagos."
"Lamarin ya afku ne da misalin karfe 11:29 na rana inda ya shiga cikin daji ba ƙaƙƙautawa."
"Jirgin na dauke da mutane 52 da kuma masu tukin jirgi uku, jami'an kwana-kwana da agaji suna kan aiki wurin ceto fasinjoji."

Kara karanta wannan

Yaki da ta'addanci: Ma'aikatar tsaro ta rabawa sojoji sababbin motocin yaki masu sulke

- Cewar majiyar

Jirgin sama ya kauce hanya a Lagos

A wani labari mai kama da wannan, an shiga fargaba yayin da jirgin sama ya kauce hanya a jihar Lagos bayan kwaso fasinjoji daga Abuja.

Lamarin ya faru ne da safiyar yau Talata 23 ga watan Afrilu a jihar yayin da jirgin ya yi saukar gaggawa tare da kauce hanya.

Rahotanni sun tabbatar da cewa lamarin ya faru ne saboda dalilin ruwan sama da aka tafka kafin faruwar tsautsayin a Lagos.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel