Murna Ta Koma Ciki Yayin da Naira Ta Ƙara Faɗuwa, Dala Ta Haura N1,500 a Najeriya

Murna Ta Koma Ciki Yayin da Naira Ta Ƙara Faɗuwa, Dala Ta Haura N1,500 a Najeriya

  • Naira na ci gaba da samun koma baya a kasuwar hada-hadar kudi ta gwamnati da ma kasuwar ƴan canji ta bayan fage
  • A jiya Jumu'a, Dalar Amaurka ta koma N1,510 a kasuwar ƴan canji yayin da kasuwar gwamnati aka yi musaya kan N1,466/$
  • Wannan dai na zuwa ne duk da matakan da CBN ya ɗauka na sayar wa ƴan canji Dala a kwanakin baya domin karya farashinta

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ƙimar kuɗin gida Najeriya watau Naira ya ƙara faɗuwa a kasuwar gwamnati yayin da aka yi musaya kan NN1,466.31/$ ranar Jumu'a, 10 ga watan Mayu.

A wani rahoto da Daily Trust ta tattara, farashin musayar Dala zuwa Naira ya karu da N40 tsakanin ranar Alhamis da Juma'a inda ya tashi daga N1,426/$.

Kara karanta wannan

Matakai 5 da Gwamnatin Tinubu ta dauka da suka jefa ‘yan Najeriya a wahalar rayuwa

Naira da Dalar Amurka.
Duk da matakan CBN darajar Naira na ci gaba da faɗuwa ƙasa kan Dala a Najeriya Hoto: Contributor
Asali: Getty Images

Kasuwar hada-hadar musayar kuɗin ƙasashen waje ta ƙasa ( NAFEM) ta tabbar da tashin Dala a tsakanin ranar Alhamis da jiya Jumu'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda Naira ta samu koma baya

Legit Hausa ta fahimci cewa farfaɗowar da Naira ta yi ya gamu da koma baya bayan wata yunƙurowa da kuɗin Najeriya suka yi kan Dala musamman a watan Afrilu.

Idan baku manta ba a lokacin sai da Dalar Amurka ta dawo kasa da N1,000 a kasuwar ƴan canji, lamarin da gwamnati ta kalla a matsayin hanyar samun sauki.

Hakan ya faru ne bayan wasu matakai da babban bankin Najeriya (CBN) ya ɗauka domin saita farashin musayar kudi a kasuwannin hada-hadar kuɗi.

Daga cikin matakan, bankin CBN ya sayar wa ƴan canji dubban Daloli a wani yunƙuri na ƙara wadatar kuɗin a kasuwannin musaya.

Kara karanta wannan

Sanatan APC ya nuna babban kuskuren Tinubu kan harajin tsaron yanar gizo

Naira ta ƙara faɗuwa a Najeriya

Yayin da Dala ta tashi zuwa N1,466.31 a kasuwar gwamnati a jiya Jumu'a, ta kuma kara tashi a kasuwar ƴan canji ta bayan fage inda aka yi musayar ta kan N1,510.

An fara hada-hada da safiyar Jumu'a a farashin N1,450 kan kowsce Dala amma kafin a tashi Dalar ta ƙara sama zuwa N1,510 a kasuwar ƴan canji, This Day ta tattaro.

Yahaya Bello ya gamu da cikas

A wani rahoton kuma Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya yi rashin nasara a yunkurin dakatar da shari'ar da ake masa kan badakalar N80bn.

Babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta yi watsi da bukatar tsohon gwamnan saboda bai halarci zaman shari'a ba ranar Jumu'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262