'Yan Bindiga Sun Kashe Babban Malamin Musulunci da Wasu Mutum 30 a Zamfara

'Yan Bindiga Sun Kashe Babban Malamin Musulunci da Wasu Mutum 30 a Zamfara

  • Yan bindiga sun kai hari kauyukan manoma a kananan hukumomin Maradun da Tsafe a jihar Zamfara ranar Alhamis da ta wuce
  • Rahoto daga yankin ya nuna cewa daga cikin waɗanda aka kashe har da wani babban malamin Musulunci, Mallam Makwashi Maradun
  • Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Zamfara, Yazid Abubakar, ya tabbatar da kai hare-haren amma ya ce bayani zai biyo baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Zamfara - Ƴan bindigan daji sun kai farmaki kauyuka biyu da aka sansu da sana'ar noma a jihar Zamfara kuna sun kashe manoma aƙalla 30.

Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa daga cikin waɗanda ƴan bindigar suka kashe har da babban malamin addinin Musulunci, Mallam Makwashi Maradun Mai Jan Baki.

Kara karanta wannan

Gwamna Fubara ya ɗauki zafi, ya canza wurin zaman majalisar dokokin jihar Rivers

Gwamna Dauda Lawal na Zamfara.
Yan bindiga sun yi ajalin manoma akalla 30 a kauyuka biyu na jihar Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Asali: Twitter

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar, ya tabbatar da kai hare-haren a wasu kananan hukumomi guda biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindiga suka kashe mutane

Wasu majiyoyi daga yankin sun shaidawa jaridar cewa lamarin ya faru ne ranar Alhamis, 9 fa watan Mayu a kauyuka biyu a Zamfara.

PR Nigeria ta kawo rahoton cewa ƴan bindiga sun kai sababbin hare-haren ne a ƙananan hukumomin Maradun da Tsafe.

Ɗaya daga cikin majiyoyin ta ce Mallam Mai Jan Baki, fitaccen malami da mutane ke girmamawa na cikin waɗanda maharan suka kashe a garin Maradun.

Ta ce bayan malamin, maharan sun kashe wani mutum ɗaya, sannan har yanzun ba a san inda biyu daga cikin ƴaƴan malamin suka shiga ba bayan harin.

Mutane sun kashe ƴan bindiga a Zamfara

An tattaro cewa ‘yan bindigar sun kashe wasu mutane uku a kauyen Gidangoga, yayin da mazauna kauyen suka kashe ‘yan bindiga 24 tare da kwato babura takwas.

Kara karanta wannan

Kotu ta kori ƴan majalisa 27 da suka sauya sheƙa zuwa APC, ta hana su aikin majalisa

Wani mazaunin garin Maradun ya ce:

"Mun tari ƴan bindigar yadda ya kamata saboda hare-hare sun zama ruwan dare a ƴan kwanakin nan a yankin Maradun, kusan kullum sai an kai hari, kauyuka da dama sun tashi saboda fargaba."

An kashe mutum 20 a kauyen Bilbis

Premium Times ta ruwaito cewa ‘yan bindigar sun kai hari kauyen Bilbis da ke karamar hukumar Tsafe, inda suka kashe fararen hula 20.

Majiyoyin yankin sun ce an kai wa manoma hari ne a lokacin da suke share gonakinsu, kuma ‘yan bindigar ba su nuna tausayi ba ko kaɗan.

Hakimin Garbadu, Alhaji Murtala Ruwan Bado a Masarautar Talata Mafara shi ma ya tsallake rijiya da baya a wani harin da ‘yan bindiga suka kai musu da yammacin ranar a kan titin Mayananchi.

Wani ɗan asalin garin Maradun, Husaini Maradun, ya shaidawa Legit Hausa cewa malamin da aka kashe na ɗaya daga cikin manyan malamansu.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi artabu da ƴan bindiga a ƙauyuka 2, sun ceto mutane da yawa a Katsina

Ya ce:

"Allah ya karɓi shahadar malam Muhammad Mai Kwanshi, yana ɗaya daga cikin manyan malaman ƙaramar hukumar Muradun da Allah ya yi wa baiwar fahimtar rabon gado.
"Sun rutsa shi a gonarsa yana aiki, suka kashe shi suka tafi da ƴaƴansa guda biyu, wannan matsalar kullum ƙara muni take, Allah ya mana magani mu samu tsaro."

Ƴan bindiga sun kai hari a Plateau

A wani rahoton kuma kun ji cewa ƴan bindiga sun kai hari kauyen Kayarda, sun kashe mutum huɗu kuma sun jikkata wasu da dama a jihar Filato.

Shugaban ƙaramar hukumar Qua’an Pan, Christopher Audu Manship, ya ce jami'an tsaro sun duƙufa da nufin kamo duk masu hannu a harin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262