Yan Sanda Sun Mamaye Bangaren Gidajen ’Yan Majalisar Dokokin Jihar Rivers

Yan Sanda Sun Mamaye Bangaren Gidajen ’Yan Majalisar Dokokin Jihar Rivers

  • Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan sanda sun tsare duka kofofin farko da na biyu na zuwa gidajen ‘yan majalisu na jihar Rivers
  • An gano cewa tun bayan da gwamnan jihar, Siminalayi Fubara ya kai ziyara bangaren gidajen ne 'yan majalisar adawa ke ta da jijiyoyin wuya
  • Duk da cewa Fubara ya bayyana dalilin kai ziyarar, jiga-jigan APC a jihar sun kasa sun tsare a wani zargi na gwanan zai rushe gine-ginen

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Rivers - Kimanin ‘yan sanda 30 dauke da makamai sun mamaye duk wata kofar shiga bangaren gidajen majalisar dokokin jihar Rivers da ke kan titin Aba, a birnin Fatakwal.

Kara karanta wannan

Gwamna Fubara ya dira majalisa yayin da ake batun yunkurin tsige shi

'Yan sanda sun mamaye bangaren gidajen 'yan majalisar dokoki a Rivers
Yayin da ake fargabar Fubara zai rusa gidajen majalisar jihar Rivers, an jibge 'yan sanda 30. Hoto: @rvhaofficial, @SimFubaraKSC
Asali: Twitter

Jaridar The Nation ta tattaro cewa ‘yan sanda sun tsare duka kofofin farko da na biyu na zuwa gidajen ‘yan majalisu domin hana shige da fice.

Lamarin ya zo ne jim kadan bayan da 'yan majalisar da Martins Amaewhule ke jagoranta suka yi ikirarin cewa gwamnan jihar na shirin ruguza gidajen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin zuwan Fubara ginin majalisar

Amma gwamnan jihar, Siminalayi Fubara, ya bayyana cewa ziyarar da ya kai rukunin gidajen a ranar Alhamis ba ta da wata mnufa ta daban.

“Shin rukunin gidajen 'yan majalisar ba ya cikin kadarorina? Shin akwai laifi a je duba yadda abubuwa ke wakana a can?
“Kuna sane da abubuwan da ke faruwa. Muna da sabon kakakin majalisa, kuma na je bangaren majalisar ne domin ganewa idona yadda abubuwa ke tafiye."

- A cewar gwamnan kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito,

Kara karanta wannan

N15tr: "Za mu binciki yadda aka ba da kwangilar titin Lagos-Calabar", Majalisa

Jiga-jigan APC sun sa ido a ginin majalisar

An tattaro cewa, biyo bayan kalaman da Amaewhule ya yi, ‘yan majalisar masu adawa da Fubara ciki har da wasu jiga-jigan APC sun yi ta zarya a rukunin gidajen majalisar har rana ta fadi.

A ranar yau Juma’a ne aka ga ‘yan sanda dauke da makamai suna kare kofar rukunin gidajen domin tabbatar da tsaron majalisar baki daya.

Majalisa ta yi doka kan safarar kwayoyi

A wani labarin, mun ruwaito maku cewa majalisar dattawa ta zartar da kudurin doka na yanke hukuncin kisa ga wadanda aka kama da laifin safarar miyagun kwayoyi.

Sanata Adamsa Oshiomhole ya gargadi majalisar da ta rika yin taka tsan-tsan wajen zartar da dokokin da suka shafi rayuwa da mutuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.