Bola Tinubu: A Karon Farko an Fitar da Bidiyon Shugaban Najeriya Tun Bayan Dawowarsa

Bola Tinubu: A Karon Farko an Fitar da Bidiyon Shugaban Najeriya Tun Bayan Dawowarsa

  • Fadar shugaban ƙasa ta saki bidiyon shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a karon farko tun bayan da ya dawo daga ƙasashen waje
  • An dai fara maganganu kan rashin ganin bidiyo ko hoton Shugaba Tinubu tun bayan da ya iso cikin ƙasar nan a ranar Laraba, 8 ga watan Mayun 2024
  • A cikin bidiyon da ɗaya daga cikin hadimansa ya sanya a shafinsa na manhajar X, an nuna shugaban ƙasan yana tafiya zuwa ofishinsa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Fadar shugaban ƙasa ta fitar da wani faifan bidiyo na shugaban ƙasa Bola Tinubu yana tafiya zuwa ofishinsa a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Hakan na zuwa ne bayan cece-kucen da aka yi ta yi saboda ƙin fitar da wani hoto ko bidiyo na dawowar shugaban ƙasar bayan makonni biyu da ya yi a ƙasar waje.

Kara karanta wannan

Gwamna Fubara ya dira majalisa yayin da ake batun yunkurin tsige shi

An fitar da bidiyon Bola Tinubu
Fadar shugaban kasa ta fitar da bidiyon Bola Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

A cikin faifan bidiyon mai daƙiƙa 28, an ga aƙalla mataimaka 15 suna raka Tinubu zuwa ofishinsa daga gidansa da ke cikin fadar Aso Rock Villa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai taimakawa shugaban ƙasan kan harkokin kafafen sadarwa na zamani, Dada Olusegun shi ne ya sanya bidiyon a shafinsa na manhajar X (wanda a baya aka fi sani da Twitter).

"Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dawo ofishinsa da safiyar yau, ya samu bayanai daga ministan sadarwa Bosun Tijjani, NCC EVC da ministan kuɗi Wale Edun, a fadar shugaban ƙasa."

- Dada Olusegun

An daɗe ba a ga Tinubu ba

Rashin nuna bidiyo ko hoton Tinubu dai tun bayan dawowarsa ya jawo ana ta cece-kuce a wasu ɓangarori na ƙasar nan.

Tun bayan da Tinubu ya hau karagar mulki shekara daya da ta wuce, mataimakansa da jami’an fadar shugaban ƙasa suna fitar da hotuna da bidiyon sowa da tashinsa daga filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Dalilin Dattawan Arewa na Adawa da Shugaba Tinubu ya bayyana

A irin wannan lokaci, manyan jami'an gwamnati kamar shugaban ma'aikatan faɗar shugaban kasa, sakataren gwamnatin tarayya, ministoci, gwamnoni da dai sauransu suna yi wa shugaban ƙasan bankwana tare da tarbarsa.

Sai dai, dawowar da shugaban ƙasan ya yi a ranar Laraba, ba a ga irin hakan ba domin babu hoto ko bidiyonsa da aka sanya.

Tinubu ya iso Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dawo Najeriya bayan ya kwashe makonni biyu a ƙasashen waje.

Shugaban ƙasan ya dawo gida Najeriya ne bayan ya ziyarci ƙasar Netherlands da halartar taron tattalin arziƙi a ƙasar Saudiyya

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng