Kebbi: Gwamna Idris Ya Naɗa Tsohon Gwamnan Jihar Shirgegen Mukami
- Tsohon gwamnan jihar Kebbi, Sa'idu Dakingari ya samu babban mukami daga Gwamna Nasir Idris a hukumar alhazai da ke jihar
- Gwamna Nasir ya nada Dakingari mukamin Amirul Hajji na wannan shekara da muke ciki domin kula da jigilar mahajjata
- Gwamnan ya kuma nada Umar Abubakar a matsayin mataimakin Amirul Hajji da kuma Alhaji Malami Shekare-Muhammad a matsayin sakatare
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kebbi - Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi ya nada tsohon gwamnan jihar, Sa'idu Dakingari mukami.
Kwamred Idris ya amince da mukamin Amirul Hajji na 2024 ga tsohon gwamnan jihar da jagorantar alhazai zuwa Saudiyya.
Wane mukami aka naɗa Dakingari a Kebbi?
Gwamnatin jihar it ta tabbatar da haka a yau Alhamis 9 ga watan Mayu a shafinta na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban hukumar alhazai a jihar, Alhaji Faruku Aliyu-Enabo ya tabbatar da haka a yau Alhamis 9 ga watan Mayu.
Faruku ya ce Mai Shari'a, Umar Abubakar shi zai kasance mataimakin Amirul Hajji na wannan shekara ta 2024 da muke ciki.
Sauran wadanda aka ba mukamai a Kebbi
Sai kuma Alhaji Malami Shekare-Muhammad wanda zai kasance a matsayin sakataren tawagar.
Sauran mambobin kwamitin sun hada da Alhaji Mohammed-Kana da Alhaji Usman Baraya da Muhammad Bello-Yakubu da sauransu.
Sanarwar ta ce daga cikin ayyukan wadanda aka daurawa nauyin akwai kula da jigilar mahajjata da ba da shawarwari domin inganta ayyukan hukumar.
Har ila yau, za su tabbatar sun bi dukkan ka'idojin hukumar da kuma alakarta da hukumar NAHCON ta kasa.
Gwamnan Kebbi zai kawo karshen 'yan bindiga
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi ya ce ba zai yi wata-wata ba domin kawo karshen 'yan yadda a jijar.
Kwamred Nasir ya ce zai tabbatar da dokar da za ta ayyana kisa kan duk masu ba 'yan bindiga bayanan sirri a jihar.
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin jaje a kauyen Tudun Bichi a karamar hukumar Danko-Wasagu kan hare-haren 'yan bindiga.
Asali: Legit.ng