Firaministan India Ya Aikewa Buhari wasikar shawari kan lafiyar motsa jiki
- Firaministan India ya turo wasika ga shugaba Buhari kan muhimmacin motsa jiki na Yoga
- Ya bayyana muhimmancin motsa jikin musamman ta fuskar yaki da kwayar cutar Korona
- Ya bayyana haka ne yayin da ake shirin bikin ranar Yoga ta duniya na majalisar dinkin duniya
Firaministan Indiya, Narendra Modi, ya rubuta wa Shugaba Muhammadu Buhari, kan fa'idodin kiwon lafiyar motsa jiki na Yoga, musamman wajen inganta garkuwar jiki da kuma taimakawa murmurewa daga Korona.
Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban kasar a cikin wata sanarwa a ranar Asabar a Abuja, ya ce Firaministan ya rubutawa shugaban na Najeriya wasikar ne yayin da duniya ke bikin ranar Majalisar Dinkin Duniya ta Yoga.
KU KARANTA: An Kame Buhunnan Kudi da Aka Shigo Dasu Daga Kasar Waje a Filin Jirgin Jihar Kano
Wa wani yankin wasikan da Legit.ng Hausa ta samo daga jaridar Vanguard, Firaministan ya ce:
“Yoga na da fa’idodi da yawa ga jiki da kuma tunani. Duk da dukkan kokari da kiyayewa, Korona na iya harbuwa ga kowane mutum. Sai dai, tsarin garkuwar jiki mai karfi na iya taimakawa wajen yaki da shi.
”Yoga na iya taimakawa wajen gina wannan garkuwan jiki, misali, ta hanyar motsa jiki da ke karfafa huhu.
”A lokaci guda, a duk fadin duniya, an tilastawa miliyoyin mutane zama a cikin gida tsawon na watanni.
”Hakn kuma ya yi illa ga lafiyar tunaninsu. Yin motsa jiki na Yoga a kai a kai na iya kuma taimaka musu su murmure.”
Da yake kara jaddada muhimmancin Yoga, Firaministan ya ce motsa jikin kan iya taimakawa wajen haduwa, gami da inganta garkuwar jikin dan adam, Daily Nigerian ta ruwaito.
Ya bayyana taken ranar bikin Yoga ta duniya na wannan shekarar
Ya lura cewa taken ranar bikin Yoga ta duniya a wannan shekara ya nuna damuwa ga koshin lafiyar mutane a duk fadin duniya.
”Matukar kokari ne tabbatar da cewa mun maida hankali kan motsa jiki gami da samun koshin lafiya.
"Ina fatan mika wasikata ta kyawawan ofisoshinku, babban godiyata ga hadin kai da kokarin da kowa ya yi don ganin bikin ranar Yoga ta duniya ya zama babbar nasara ga al'ummar ku a kowace shekara.
”Na tabbata cewa wannan shekarar ba za ta bambanta ba.
Ya kara da cewa:
"Da fatan za ku karbi fatan alheri na zuwa gare ku, danginku da kuma 'yan kasar ku, don samun koshin lafiya da walwala."
KU KARANTA: Yadda 'Yan Bindiga Suka Yi Amfani da Motar Mahaifin Dalibi Wajen Sace Daliban Kebbi
A wani labarin, Jakadan Koriya ta Arewa a Najeriya Chi Tun Chon Hu, ya ce gwamnatinsu ta ba da fifiko wajen bunkasa alakar kasashen biyu, BBC ta ruwaito.
Ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Abuja lokacin da ya ziyarci Shugaban Jam’iyyar APC na kasa.
Ya ce ya lura cewa Najeriya da Koriya ta Arewa sun yi tarayya a abu daya, inda ya ce rajistar jam’iyya da jam’iyya mai mulki a kasar ta APC ta yi a kwanan nan babbar nasara ce.
Asali: Legit.ng