Dalilin Dattawan Arewa na Adawa da Shugaba Tinubu Ya Bayyana

Dalilin Dattawan Arewa na Adawa da Shugaba Tinubu Ya Bayyana

  • Farfesa Khalifa Dikwa ya yi magana kan dalilin da ya sa Dattawan Arewa suke adawa da gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu
  • Shugaban na ƙungiyar Dattawan Borno ya bayyana cewa da yawa daga cikin muƙaman da Tinubu ya ba da, baragurbi ya ɗauko ya naɗa
  • Ya kuma buƙaci shugaban ƙasan da ya gaggauya umartar babban bankin Najeriya (CBN) ya soke sabon harajin kaso 0.5% da ya ɓullo da shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban ƙungiyar dattawan Borno, Farfesa Khalifa Dikwa, ya bayyana dalilin Dattawan Arewa na yin adawa da Shugaba Bola Tinubu.

Khalifa Dikwa ya bayyana cewa Dattawan Arewa ba su jin daɗin Bola Tinubu ne saboda yadda ya zaɓi baragurbi ya ba su muƙamai da kuma manufofinsa na tsawwalawa jama'a.

Kara karanta wannan

"Ba za su iya ba": Sanata Ibrahim ya jero ministocin da ya kamata Bola Tinubu ya kora

Dalilin Dattawan Arewa na adawa da Tinubu
Farfesa Khalifa Dikwa ya yi magana kan nade-naden Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Mai sharhin kan al'amuran siyasan ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da tashar Channels tv a shirinsu na 'Politics Today' a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Dattawan Arewa ke adawa da Tinubu?

Ya bayyana cewa Dattawan Arewa ba su jin daɗi ne saboda manufofin na Shugaba Tinubu sun shafi yankin Arewa ne gaba ɗaya.

"Da yawa daga cikin waɗanda ya naɗa ko dai baragurbi ne ko ba a sanya su inda ya dace ba. Da yawa daga cikin naɗe-naɗen na sa an fifita wani yanki ne."
"Har Dattawan Kudu kamata ya yi su nuna ɓacin ransu saboda Najeriya ba Legas ba ce kaɗai."

- Farfesa Khalifa Dikwa

Tinubu: Dattijon Arewa ya soki harajin 0.5%

Dattijon ya kuma soki harajin kaso 0.5% na tsaro ta yanar gizo da babban bankin Najeriya (CBN) ya ɓullo da shi kwanan nan.

Kara karanta wannan

Jirgin shugaba Tinubu ya iso Najeriya bayan kwashe makonni a kasashen waje

Ya kuma buƙaci shugaban ƙasan da ya gaggauta umartar babban bankin ya dakatar da aiwatar da wannan sabuwar dokar.

A kalamansa:

"Yanzu ba lokacin yin hakan ba ne, ba daidai ba ne. Meyasa suke son tunzura mutanen ƙasar nan? Sun jure da yawa haka nan."

Nadamar Dattawa Arewa kan Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar Dattawan Arewa (NEF) ta nuna nadamarta kan yadda yankin ya ba da ƙuri'u masu yawa ga Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2023.

Ƙungiyar ta bayyana cewa yankin Arewacin Najeriya ya yi kuskure wajen zaɓen Shugaba Tinubu inda ts yi nuni da cewa nan gaba dole a sake lale wajen zaɓen ɗan takara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng