EFCC Ta Sanya Ranar Miƙa Ministan Buhari da 'Yarsa a Gaban Kotu Kan Zargin N2.7bn
- Hukumar yaki da cin hanci ta EFCC za ta gurfanar da tsohon ministan jiragen sama, Hadi Sirika a ranar Alhamis 9 ga watan Mayu
- Hukumar na zargin tsohon Ministan Buhari da kuma 'yarsa mai suna Fatima da badakalar N2.7bn da wasu mutane biyu
- Za a gurfanar da Sirika ne a karon farko a gaban Babbar Kotun Tarayya karkashin jagorancin Sylvanus Oriji a Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Hukumar EFCC ta sanya ranar gurfanar da tsohon ministan jiragen sama, Hadi Sirika a gaban kotu.
Hukumar ta tabbatar da gobe Alhamis 9 ga watan Mayu a matsayin ranar gurfanar da shi a gaban Babbar Kotun Tarayya.
Wane zargi EFCC ke yi kan Sirika?
Ana zargin Sirika da 'yarsa mai suna Fatima da kuma wasu mutane biyu kan badakalar N2.7bn, kamar yadda rahoton Punch ya tabbatar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan shi ne karon farko da za a gurfanar da Ministan a gaban kotu karkashin jagorancin Mai Shari'a, Sylvanus Oriji na Babbar Kotun Tarayya, cewar Peoples Gazette.
Sirika zai gurfana a gaban kotu da 'yarsa mai suna Fatima da Jalal Hamma da kuma Al-Duraq Investment Kan Zargin badakala kwangiloli.
Zarge-zarge da EFCC ke yi wa Sirika
Tsohon Sanatan zai gurfana ne bayan zargin badakalar wasu kudi yayin da ya ke shugabancin ma'aikatar jiragen sama.
Badakalar ta shafi wasu kwangiloli karkashin ma'aikatarsa da ake zargin an yi baba-kere da su a lokacin.
Tsohon Ministan ya fito ne daga jihar Katsina wanda tsohon shugaba kasa, Muhammadu Buhari ya ba shi mukamin Ministan jiragen sama.
EFCC ta bukaci koyi da Yar'adua
A wani labarin shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede ya magantu kan halayen marigayi Umaru Musa Yar'adua.
Olu Olukoyede ya ce inama ace shugabannin Najeriya za su yi koyi da halayen marigayin yayin da ya mulki jihar Katsina da kuma Najeriya baki daya.
Wannan na zuwa ne yayin taron tunawa da marigayi tsohon shugaban kasar a ranar Litinin 6 ga watan Mayu a birnin Tarayya Abuja.
Asali: Legit.ng