Kujerar PDP Na Kasa: Kotu Ta Yi Hukunci Kan Tsige Shugaban Jam’iyya
- BBabbar kotun tarayya da ke Abuja ta haramtawa jam'iyyar PDP daga nada sabon shugaban jam'iyyar ko kuma ta tsige Umar Damagum
- A ranar 2 ga watan Mayu, Umar El-Gash Maina da Zanna Mustapha Gaddama suka roki kotun da ta hana PDP ta tsige Damagum
- An tattaro cewa magoya bayan Atiku Abubakar ne suke neman tsige Damagun saboda zargin yana yi wa Nyesome Wike aiki
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dakatar da jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) daga tsige Umar Damagum a matsayin shugaban riko.
Umar El-Gash Maina da Zanna Mustapha Gaddama ne suka shigar da kara gaban kotun mai lamba FCH/ABJ/CS/579/2024 a ranar 2 ga watan Mayu.
Wadanda ake karar su ne PDP, kwamitin ayyuka na kasa (NWC), kwamitin shugabanni na kasa (NEC), kwamitin amintattu (BoT) da hukumar INEC, in ji rahoton The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotu ta hana PDP tsige Damagum
Alkalin kotun, Mai shari'a Peter Lifu ya dakatar da wadanda ake kara daga tsige Damagun ko maye gurbinsa da wani har sai an kammala shari'ar.
"Kotu ta haramtawa wadanda ake kara daga nada wani shugaba ko tsige Amb. Umar Illiya Damagum daga kujerar shugaban riko har sai kotu ta yi hukuncin karshe.
"Hakazalika, wadanda suka shigar da karar su kwana da sanin cewa za a ci su tara idan har a karshe kotu ta gano cewa bai kamata su shigar da irin wannan bukatar a gaban kotu ba."
- A cewar Mai shari'a Peter Lifu.
Kotun ta dage shari'ar zuwa ranar 14 ga watan Mayu domin fara sauraron karar.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Damagun ya zama shugaban riko na jam'iyyar PDP bayan dakatar da Iyorchia Ayu da aka yi a watan Maris din 2023.
Magoya bayan Atiku ke adawa da Damagun
Kafin babban taron shugabannin jam'iyyar, mambobin PDP da ke goyon bayan Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa, sun nuna adawa ga Damagun.
Sun zarge shi da yin aiki karkashin umarnin Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja, wanda suke ganin hakan tamkar zagon kasa ne ga jam'iyyar.
Wadanda ke neman a tsige Damagun sun kuma yi ikirarin cewa akwai bukatar wani daga shiyyar Arewa ta tsakiya ya karbi ragamar jam'iyyar domin karasa wa'adin Ayu.
Tsige Fubara: PDP ta gargadi APC
A wani labarin kuma, jam'iyyar PDP ta gargadi APC daga furta kalaman da ka iya tunzura al'ummar jihar Rivers yayin da APC ta yi kira da a tsige Gwamna Siminilayi Fubara.
PDP ta kuma yi kira ga Sufeta Janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun, da ya ja kunnen shugabannin APC na jihar Rivers kan kalamansu domin gujewa ta da husuma.
Asali: Legit.ng