Gwamnatin Tarayya Ta Yi Martani Kan Zargin Neman Cin Hancin $150m a Hannun Binance
- Gwamnatin tarayya ta yi watsi da zargin neman cin hancin Dala miliyan 150 da kamfanin Binance ya yi kan wasu jami'an gwamnati
- Mohammed Idris, ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a na ƙasa, ya bayyana zargin a matsayin wata dabara ta karkata akalar tuhumar da kamfanin ke fuskanta a gaban kotu
- A cewar ministan, mafita ɗaya tilo ga kamfanin na kirifto ita ce ya bi ƙa’idoji da dokokin da ke jagorantar harkokin kasuwanci a ƙasa mai cikakken iko kamar Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta mayar da martani kan zargin da kamfanin Binance ya yi na cewa wasu jami'an gwamnati sun buƙaci ya ba su cin hanci.
Kamfanin ya yi zargin cewa jami'an sun buƙaci a ba su cin hancin $150m na kirifto domin a wanke shi daga zarge-zargen da ake yi masa.
Cin hanci: Gwamnati ta karyata Binance
Gwamnati ta yi martanin ne a wata sanarwa a shafin X mai ɗauke da sa hannun Rabiu Ibrahim, mataimaki na musamman ga ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama'a na ƙasa, Mohammed Idris.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Najeriya ta ce Binance ba zai iya wanke kansa ba ta hanyar ƙoƙarin ɓata sunan ƙasar nan.
Yadda Binance zai wanke kansa
Gwamnatin tarayya ta ce mafita ɗaya tilo ga kamfanin na kirifto ita ce ya bi ƙa’idoji da dokokin da ke jagorantar harkokin kasuwanci a ƙasa mai cikakken iko kamar Najeriya.
A wani rubutu da ya yi, shugaban kamfanin Binance, Richard Teng, ya yi zargin cewa gazawar kamfanin wajen ba da cin hanci ne ya sanya aka kama tare da gurfanar da jami'ansa a Najeriya.
Me gwamnati ta ce kan zargin Binance?
Sai dai, gwamnatin tarayya, a cikin martaninta, ta ce shugaban na Binance ya yi zargi na ƙarya a rubutun na sa.
Gwamnatin tarayya ta ce wannan iƙirarin na kamfanin Binance ba shi da hujja madogara kuma ƙoƙari ne kawai na ɓata sunan gwamnatin Najeriya.
Sanarwar ta ce shugaban na Binance yana so ne ya ɓoye munanan laifukan da kamfanin ke fuskanta a Najeriya.
$150m: Batun zargin Binance
A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar wakilai ta yi martani kan zargin karɓar cin hanci daga kamfanin kirifto na Binance da ake yadawa.
Majalisar ta ƙaryata rade-radin inda ta ce babu ƙamshin gaskiya kan zargin da kamfanin ya yi na cewa an buƙaci ya bayar da cin hanci.
Asali: Legit.ng